Da duminsa: An tsinci jirgin yakin sojin saman Najeriya a wajen Maiduguri

Da duminsa: An tsinci jirgin yakin sojin saman Najeriya a wajen Maiduguri

- An gano jirgin yakin sojojin saman Najeriya da ya bace a yankin arewa maso gabas

- An ga jirgin ne a karamar hukumar Konduga dake da kusanci da garin Maiduguri a Borno

- Amma har a halin yanzu, ba san inda matukan jirgin biyu suke ba ko da aka ga jirgin

Alamu sun nuna cewa jirgin yakin sojojin Najeriya da ya bace an gan shi a karamar hukumar Konduga dake jihar Borno mai nisan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jihar.

Duk da hukumar rundunar sojin kasan bata riga ta tabbatar da wannan cigaban ba, majiyoyi a ranar Juma'a sun ce an ga jirgin yakin na shawagi a kauyukan Goni Kurmiri da Njimia bayan ragargaza 'yan ta'adda a Sambisa da yayi.

Majiyoyin sun ce, har yanzu ba a samu labarin inda matukin jirgin da abokin aikinsa suke ba, Channels TV ta wallafa.

KU KARANTA: Ruwan wuta aka yi mana na minti 15, Soludo ya bada labarin karonsu da 'yan bindiga

Da duminsa: An tsinci jirgin yakin sojin saman Najeriya a wajen Maiduguri
Da duminsa: An tsinci jirgin yakin sojin saman Najeriya a wajen Maiduguri. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan Obasanjo ya cakare tare da gwangwajewa tamkar matashin saurayi

Hukumar sojin saman ta sanar da cewa jirgin yakin sojojin ya bace a ranar Laraba da yammaci yayin da yake ayyukan yau da kullum na taimakawa dakarun sojin kasa a yankin arewa maso gabas.

A ranar Juma'a ne rundunar ta sanar da cewa akwai yuwuwar cewa jirgin saman hatsari yayi.

Kamar yadda takardar da rundunar ta fitar daga hannun daraktan hulda da jama'a da yada labarai, Air Commodore Edward Gabkwet, jirgin yana dauke da matuka biyu kuma ya bace a jihar Borno.

A wani labari na daban, sojojin Najeriya sun bazama neman matuƙan jirgin sama da suka ɓata bayan an nemi wani jirgin yaƙi sama ko ƙasa ba a gani ba bayan jirgin ya tafka hatsari a dajin Sambisa dake arewa maso gabas na Najeriya.

HumAngle ta fahimci yadda sojojin suka rikice suna neman sojojin lungu da saƙon dajin Sambisa. Yanzu haka an zarce sa'o'i 24 tun bayan faruwar lamarin.

Dajin Sambisa babban daji ne wanda yankin Boko Haram ɗin Sheƙau suka mamaye shi kuma ana zargin sune suka kaiwa jirgin farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel