Shugaban kasan Japan ya nada 'ministan kadaici' bayan hauhawar kashe kai
- Shugaban kasar Japan yayi nadin ministan kadaici a kokarin shawo kan masu kashe kansu a kasar
- An gano cewa an kirkiro wannan mukamin a kasar ne a watan Fabrairu don gujewa masu killace kansu su kashe kansu
- A kiyasin da aka yi a 2020, yawan wadanda suka kashe kansu sun fi yawan wadanda cutar korona ta kashe a kasar
Shugaban kasar Japan ya nada ministan kadaici a kokarinsa na rage kadaici da hana kebance kai a tsakanin mazauna kasar domin rage yawan masu kashe kansu.
Kamar yadda The Japan Times ta ruwaito, Firayim minista Yoshihide Suga ya kirkiro kujerar a watan Fabrairu bayan Ingila ta kirkiro mukamin a shekarar 2018.
Kiyasi daga rundunar 'yan sandan kasar ya nuna cewa mutum 20,919 ne suka kashe kansu a 2020, karin mutum 750 da aka samu a shekarar da ta gabata. Kamar yadda aka gano, yawan wadanda ke kashe kansu sun fi a mata da matasa.
KU KARANTA: Kada ku bar masu gulma da tsegumi su raba kawunanmu, Buhari ga 'yan Najeriya
KU KARANTA: 'Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gidan yari, Pantami
The Times ta ce Japan ta san da kadaicin da ake kira da kodukushi ko kuma 'mutuwar kadaici' an saba ganinsu a Japan. Jama'a na mutuwa a gidajensu kuma ba a sanin sun mutu sai bayan wani lokaci.
An gano cewa Japan ce kasar da take da mutane masu shekaru 60 zuwa sama da suke jin basu da wanda za su komawa a lokutan bukata.
A watan Oktoba, Japan ta fuskanci mutuwar jama'a wadanda suka kashe kansu fiye da yawan wadanda cutar korona ta kashe a 2020.
A watan Oktoban 2020 kadai, an samu mutum 2,153 da suka kashe kansu a Japan yayin da cutar korona ta kashe mutum 1,765 a dukkan shekarar.
A wani labari na daban, Charles Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace a harin da ƴan bindiga suka kai masa, sai da suka yi ta musayar wuta da ƴan sanda na tsawon mintuna 15.
Jaridar The Cable ta bayyana yadda wasu ƴan bindiga suka kaiwa Soludo farmaki a wani dakin taro dake Isuofia, ƙaramar hukumar Aguata dake jihar Anambra a ranar Laraba.
Wasu ƴan sanda guda 3 da suke kula da lafiyarsa sun rasa rayukansu a harin, sannan sun yi garkuwa da wani kwamishinan jihar, Emeka Ezenwanne.
Asali: Legit.ng