Gwamna El-Rufai zai hukunta duk wanda ya yi sulhu da ‘Yan bindiga a jihar Kaduna
- Gwamnatin Kaduna za ta kafar wando daya da masu satar Bayin Allah
- Yanzu an haramta magana ko a biya ‘yan bindiga kudin fansa a Kaduna
- Samuel Aruwan ya ce za a hukunta duk wanda aka samu ya saba doka
Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu ya na magana da wadanda su ka sace yaran makaranta 39 da aka sace.
Kwanakin baya wasu miyagun ‘yan bindiga su ka shiga babbar makarantar gandun dabbobi da ke garin Afaka, jihar Kaduna, su ka sace dalibai kusan 40.
Gwamnatin Kaduna ta ce za a hukunta duk wadanda aka kama su na neman biyan bukatan wadannan ‘yan bindiga saboda a fito masu da ‘ya ‘yansu.
KU KARANTA: Gwamnati ta gayyaci Malaman makaranta a zauna
Kwamishinan harkar tsaron cikin-gida na Kaduna, Samuel Aruwan, ya fitar da jawabi a ranar Lahadi, inda ya gargadi masu shirin biyan kudin fansa.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Samuel Aruwan ya ce babu maganar biyan kudin fansa ko a shiga wata yarjejeniya da miyagun ‘yan bindigan.
Jawabin kwamishinan ya ce: “Za a kama duk wanda aka samu da laifin yin wadannan ko ta wace irin hanya ce, sannan kuma a hukunta shi yadda ya kamata.”
Aruwan ya ke cewa an fitar da wannan sanarwa ne saboda rade-radin da ake yi na cewa na nada wasu da za su yi sulhu da ‘yan bindiga a madadin gwamnati.
KU KARANTA: Gaskiyar abin da ya faru tsakani na da Shugaban CCT – Maigadi
Wannan jawabi ya karkare da cewa: “Gwamnatin jihar Kaduna ta na so ta yi karin-haske cewa ba a nada wasu da za su yi magana a madadin gwamnati ba.”
Amma iyayen yara sun yi tir da wannan jawabi da aka fitar, su ka zargi gwamnati da halin ko-in-kula.
Shugaban kungiyar iyayen yaran da aka sace, Sam Kambai, ya ce za su yi duk abin da za su iya na ganin sun kubuto da ‘ya ‘yansu daga hannun masu garkuwa.
A gefe guda, kun ji cewa iyayen daliɓan da aka sace a kwalejin koyar da aikin noma da gandun dabbobi dake jihar Kaduna sun ce sun shirya zama da ƴan bindiga.
Rahotanni sun wadannan mutane da aka sace masu yara za su nemi su bada duk abin da ake bukata domin kuɓutar da rayuwar ƴaƴansu daga hannun miyagu.
Asali: Legit.ng