Tashin Hankali! Wasu yan bindiga sun Kashe 'yan kasuwa 7 Yan Arewa a jihar Imo

Tashin Hankali! Wasu yan bindiga sun Kashe 'yan kasuwa 7 Yan Arewa a jihar Imo

- An shiga cikin yanayin tashin hankali a jihar Imo bayan kisan wasu yan kasuwa 7 yan Arewa da aka yi a cikin kwana biyu

- Shaidun gani da ido sun tabbatar a aukuwar lamarin, kuma sun ce mutanen da aka kashe sun daɗe suna rayuwa a yankin ba tare da wata matsala ba

- Sai dai rahotanni sun bayyana cewa waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin baƙi ne don ba'a gane ko suwaye ba

Ana cikin yanayin ɗar-ɗar da da tashin hankali a jihar Imo bayan wani kisa da akai ma yan kasuwa 7 yan arewa a jihar.

Rahoton jaridar Dailytrust ya bayyana cewa an kashe mutanen ne a harbi daban-daban a garin Orlu da Umuaka dake ƙaramar hukumar Njaba tsakanin ranar Jumu'a da Asabar.

KARANTA ANAN: WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan

Ya yin da yake bayyana yadda abun ya faru ga manema labarai, wani shaidan gani da ido, Harisu Umaru Ishiaku, ya ce waɗanda suka aikata kisan sunzo a cikin kayan sojoji su ka farmaki mutanen a kasuwar Afor Umuaka da misalin ƙarfe 8:30 na dare.

Ya ce, huɗu daga cikin waɗanda aka kashe suna da shekaru tsakanin 30 zuwa 45 kuma suna rayuwar su a wannan yankin na tsawon shekaru.

Sai dai ana zargin waɗanda suka kawo harin baƙi ne, ya kuma ce babu wata matsala tsakanin al'ummar yankin Umuaka da mutanen da aka kashe ɗin.

A cewar shugaban ƙungiyar hausawa yan kasuwa, Mallam Ibrahim Abdulkadir, an kai harin farko ran Jumu'a lokacin da mutane huɗu masu siyar da Suya suke shirin tashi a ranar.

Ya ce ba zato babu tsammani sai wasu yan bindiga suka ƙariso wajen a cikin mota, suka buɗe musu wuta, suka harbe su a jikinsu.

Tashin Hankali! An Kashe 'yan kasuwa 7 Yan Arewa a jihar Imo
Tashin Hankali! An Kashe 'yan kasuwa 7 Yan Arewa a jihar Imo Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

Ya kuma ƙara da cewa, a yanayi irin wancan, yan bindigan suka sake kawo hari a kasuwar Umuaka, inda suka sake buɗewa hausawa yan kasuwa wuta.

Abdulƙadir ya ce, yanzu yan kasuwa hausawa na rayuwa cikin tsoro a garin Orlu, ya ƙara da cewa wasu ma har sun bar garin zuwa Owerri.

A bayaninsa Abdulƙadir yace:

"Maganar gaskiya wannan abun ya fara ne tun biyu ga wannan watan, an kira ni a waya an faɗa mun wasu yan bindiga a motar Sienna sun kashe masu siyarda suya uku."

"Muna ƙoƙari akan wannan lamarin sai kuma aka sace kirana akace an sake kashe wasu mutum huɗu."

KARANTA ANAN: Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, El-Rufa'i ya maida Martani

Wakilin Dailytrust ya gano cewa an ɗauki gawarwakin waɗanda aka kashe an tafi dasu Owerri don yi musu jana'iza.

Babban mai baiwa gwamnan jihar shawara kan al'amuran mutanen arewa, Hon. Sulaiman Ibrahim Sulaiman, ya ce gwamnatin jihar da dukkan hukumomin tsaron sun shiga cikin lamarin.

Ya yin da yake kira da akwantar da hankulla, Sulaiman ya ce gwamnan jihar ya damu d lamarin da ya faru.

Duk wani yunƙuri na jin ta bakin mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar ya ci tura, saboda an kasa samun wayarshi.

A wani labarin kuma Sheikh Gumi ya jagoranci Malamai sun kaima tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo Ziyara

Shahararren malaminnan, Sheikh Gumi ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da safiyar yau don tattaunawa da shi.

Rahotanni sun tabbatar da zuwan malamin tare da wasu malaman addini kuma a yanzun haka suna tsakar tattaunawa da Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel