Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas

Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas

- Hare-haren makiyaya na baya-bayan nan a fadin yankin Igbo ya haifar da tashin hankali a yankin kudu maso gabas

- Daruruwan mutane sun mutu saboda yawan hare-haren da makiyaya ke kaiwa manoma

- Wata kungiyar mata a yankin ta bukaci hukuma data shawo kan hare-haren ko kuma su hau kan titi tsirara a duk fadin kasar Igbo

Ndinne Igbo, wata kungiyar zamantakewar mata, ta yi barazanar cewa mambobinta za su yi tattaki tsirara a fadin kasar ta Igbo don nuna rashin amincewa da kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankin idan har hukumomin da abin ya shafa ba su shawo kan lamarin ba.

Yankin kudu maso gabas na fama da rikice-rikicen makiyaya a makwannin da suka gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle na shirin komawa APC gabannin zaben 2023

Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas
Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Kungiyar ta yi Allah-wadai da harin makiyaya da ya auku a jihohin Enugu da Ebonyi, inda ta koka kan yadda yara ‘yan kabilar Ibo da dama suka zama cikin mummunan harin.

Kungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran ta, Misis Beatrice Chukwubuike, a ranar Asabar, 3 ga Afrilu kuma Legit.ng ta gani, ta yi kira ga shugabannin Najeriya da na Ibo da su kamo wannan mummunan lamarin kafin ya tabarbare.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya nuna bakin ciki yayinda yake juyayin rashin kakakin Afenifere Yinka Odumakin

A gefe guda, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Ista don yin addu’a ga hadin kan Najeriya da kuma dawowar zaman lafiya a kasar.

A sakonsa na Ista ga 'yan Najeriya, Atiku ya tuno da yadda kwayar cutar Coronavirus ta gurgunta harkoki sosai a yawancin kasashen duniya a shekara guda da ta gabata.

Har ila yau tsohon Mataimakin Shugaban kasar, ya jinjina wa ma’aikatan lafiya wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen yaƙi da cutar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel