Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, El-Rufa'i ya maida Martani

Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, El-Rufa'i ya maida Martani

- Gwamnan Kaduna ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta cewa gwamnatinsa ta naɗa masu shiga tsakani don tattaunawa da yan bindiga

- Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa nan nan akan bakar ta na cewa ba maganar tattaunawa kuma ba bu biyan kuɗin fansa

- Kwamishina tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ne ya bayyana haka a yau Lahadi

Gwamna Nasir Ahmad El-rufa'i na jihar Kaduna ya musanta labarin da ake yaɗawa cewa ya naɗa tawagar da zasu jagoranci tattaunawa da 'yan bindiga.

KARANTA ANAN: Bikin Ista: Ministan Tsaro ya roƙi yan Najeriya da su saka sojojin ƙasar nan cikin Addu'a

Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana haka a yau Lahadi.

Ya ce gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Ahmad Elrufa'i ta ji labarin ana yaɗa jita-jita a kafar sada zumunta cewa gwamnatin ta naɗa wakilai da zasu tattauna da yan bindiga a madadinta.

A jawabin da kwamishinan ya yi a madadin gwamnan ya ce:

"Gwamnatin Kaduna na kara tabbatar da cewa bata naɗa kowa ba dan shiga tsakani da yan bindiga."

Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, El-Rufa'i ya maida Martani
Duk Soki Burutsu ne, Bamu naɗa kowa dan tattaunawa da yan Bindiga ba, El-Rufa'i ya maida Martani Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga- zangar tsirara a fadin kudu maso gabas

A maganarsa ya ce gwamnatin Kaduna na nan akan bakarta na ba zata tattauna da yan bindiga ba.

"Gwamnatin mu ba zata tattauna da yan bindiga ba haka kuma bazata biya kudin fansa ba.Duk mutumin da aka kama yana haka da sunan wakilin gwamnati za'a hukunta shi kamar yadda doka ta tanazar." a cewar kwamishinan.

A Kwanakin baya dai, Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata tattauna da yan bindiga ba kuma ba zata biya wani ɗan bindiga kuɗi da sunan kuɗin fansa ba.

A wani labarin kuma Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna, a ranar Asabar, ta bayyana cewa jami'an tsaro sun ceto akalla mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar.

A jawabin da kwamishanan harkokin cikin gida da tsaron jihar, Samuel Aruwan, ya saki, ya ce hukumar yan sandan jihar ce ta baiwa gwamnatin jihar rahoton ceto mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel