WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan

WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan

- Ƙungiyar Lafiya ta duniya (WHO) ta gargaɗi musulmai da kiristoci kan gudanar da bikukuwan addinin su dake ƙaratowa

- WHO ta ce kada mutane su manta da ƙa'idojin kariya daga cutar korona a ya yin gudanar da bukukuwan su

- Ƙungiyar ta shawarci da su gudanar da bukukuwansu a gida tare da mutanen da suka saba rayuwa da su.

Kwanaki kaɗan kafin zuwan watan Ramadan da kuma na ista, ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta gargaɗi musulman duniya kan dokokin kare yaɗuwar korona.

KARANTA ANAN: Yajin aikin Likitoci: Sabon jariri ya mutu a asibiti sakamakon rashin Likita

WHO ta ce ya kamata ƙasashen da suke fuskantar ƙaruwar masu kamuwa da cutar su ɗage waɗannan bukukuwan ko kuma su rage yawan jama'an da zasu haƙarci wurin.

Ƙungiyar ta ce duk wani taron addini da za'ai a fili wanda zai tara jama'a, kamata ya yi a ƙayyade jama'an da zasu harci wurin.

Haka kuma WHO ta ce duk wanda ya halarci wajen to ya kiyaye ka'idojin kare yaɗuwar cutar COVID19, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Ƙungiyar ta shawarci al'umma da cewa, zai fi ma jama'a kyau su yi bikinsu a cikin gida tare da waɗanda suke rayuwa tare. Su guje ma haɗuwa da sabbin mutane musamman waɗanda basu da lafiya.

WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan
WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan Hoto: @Channelstv
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Ana binciken Aminu Ado Bayero da Mukarrabansa da badakalar Naira Biliyan 1.3

"Duk wani taro da zai haɗa mutane kala daban-daban to yanada hatsari," cewar WHO.

Masana na tsoron mutane za su iya aje ƙa'idojin kariya daga kamuwa da cutar COVID19 a ya yin da suke gudanar bikin addinin su.

A kwanaki kaɗan masu zuwa kiristoci zasu gudanar da bikin ista, haka kuma ana sa ran musulmi za su fara ibadar azumin ramadan a ran 13 ga watan Afrilu.

A wani labarin kuma Zakakuran sojin Najeriya sun sheke 'yan ta'adda 7 da suka kaiwa tawagar Zulum hari

Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno farmaki a ranar Juma'a, 2 ga watan Afirilu kan titin Monguno zuwa Nganzai.

Jami'an tsaron sun nuna jarumtarsa ta hanyar kashe 'yan ta'addar guda 7 bayan sunyi musayar wuta.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel