Mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan, Saudiyya

Mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan, Saudiyya

- Hukumar kasar Saudiyya na shirin kara yawan Musulmi da za su yi aikin Umrah a azumin bana

- Saudiyya dai ta rage yawan masu shiga kasar don gudanar da aikin Umrah a bara sakamakon barkewar annobar korona

- Mataimakin ministan kula harkokin aikin hajji, Abdulfattah Mashat ya sanar da matakan da aka dauka wanda zai bayar da damar yin hakan

Rahotanni sun kawo cewa kasar Saudiyya na shirin kara yawan mutane da ke son yin aikin Umrah a watan azumin Ramadan wanda ya rage saura yan kwanaki.

Tun da fari dai hukumar kasar Saudiyya ta rage yawan mutanen da ta yarda su gudanar da aikin Umrah sakamakon barkewar annobar korona a duniya.

KU KARANTA KUMA: Ku tayani da addu'a, ina cikin kangin rayuwa har ina ji kamar na kashe kaina, Ummi Zeezee

Mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan, Saudiyya
Mutane da dama za su iya yin umrah lokacin Ramadan, Saudiyya Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa mataimakin ministan kula harkokin aikin hajji, Abdulfattah Mashat, ya sanar da cewa za a yi wa dukkanin ma’aikatan da ke kula da masallacin Ka’aba rigakafin cutar ta korona.

Ya ce wannan matakin zai ba musulmi da dama damar gudanar da aikin Umrah musamman kasancewar an fi zuwa a lokacin azumin watan Ramadan.

Mashat ya jaddada cewa kwamitoci na musamman da aka kafa za su tabbatar da cewa an yi amfani da matakan kiwon lafiya a masallatan harami biyu na Makka da Madina.

Annobar korona ta tilastawa wa Saudiyya dakatar da yin Umrah a watan Maris din bara. Kuma an rage yawan mutanen da suka gudanar da aikin hajji sosai a shekarar.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas

A baya mun ji cewa manyan Limaman Harami sun hadu domin tsara Jadawalin sallolin Taraweeh da Tahajjud na watan Ramadana.

Tuni dai hukumomin kasar ta Saudiyya suka fitar da jerin sunayen manyan limaman da za su jagoranci bayar da sallolin Tarawi da Tuhajjud a masallacin Harami da ke kasa mai tsarki a azumin wannan shekarar ta 2021.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wallafa da shafin Twitter na Haramain Sharifain ya yi a ranar Laraba, 24 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel