Bikin Ista: Ministan Tsaro ya roƙi yan Najeriya da su saka sojojin ƙasar nan cikin Addu'a

Bikin Ista: Ministan Tsaro ya roƙi yan Najeriya da su saka sojojin ƙasar nan cikin Addu'a

- Ministan tsaron ƙasar nan, Bashir Magashi, ya taya mabiya addinin kirista murnar zagayowar bikin ista na wannan shekarar

- A saƙon taya murnanr, ministan ya roki kiristoci da su yi amfani da wannn damar wajen saka sojoji a addu'a su kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan

- Ya ƙara da tabbatar wa yan Najeriya cewa sojoji da dukkan jami'an tsaron ƙasar nan suna matuƙar ƙoƙari wajen daƙile matsalar tsaro.

Ministan tsaron ƙasar nan, Bashir Magashi, ya roƙi kiristoci da su yi ma sojojin ƙasar nan addu'a don kawo ƙarshen ta'addanci.

KARANTA ANAN: Wasu fitattun kasar nan ne ke son a raba Najeriya, talakawa babu ruwansu, Ahmad Lawan

A wani jawabi da ya fitar ran Asabar ta hannun mai taimaka ma ministan kan harkokin yaɗa labarai, Mohammad Abdulkadri, Magashi ya roƙi mabiya addinin kirista da su yi amfani da wannan damar ta bikin ista su roƙi dawowar zaman lafiya a ƙasar nan.

Ministan ya ce, lokacin biki ista lokaci ne da yakamata mu roƙi taimakon Ubangiji ya shigo lamurran mu don samun hanyoyin magance ƙalubalen tsaro da muke fama da shi.

Ya kuma yi kira ga bukatar da muke dashi na yin ayyuka nagari, biyayya ga dokokin ƙasa, da kuma babbar bukatar Najeriya na zama ƙasa guda ɗaya.

Ministan ya roƙi mabiya addinin kirista da su saka sojojin ƙasar nan a addu'o'insu don samun nasara a yaƙin da suke yi.

Bikin Ista: Ministan Tsaro ya roƙi yan Najeriya da su saka sojojin ƙasar nan cikin Addu'a
Bikin Ista: Ministan Tsaro ya roƙi yan Najeriya da su saka sojojin ƙasar nan cikin Addu'a Hoto: @HQNigerianarmy
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Shugaban Majalisar dattijai ya gwangwaje yan kasuwar da gobara ta shafa a Jihar Yobe da abin Arziƙi

Haka kuma don su samu nasarar dawo da dauwamammen zaman lafiya, su ceto ƙasar mu daga mummunan yana yin rashin tsaro da take ciki.

Ministan ya kuma kira yi sojin ƙasar nan da su cigaba da matsawa a yaƙin da suke yi, kuma su haɗa kansu wajen yaƙar maƙiyan zaman lafiyar ƙasar nan.

Daga ƙarshe, Magashi ya tabbatar ma yan Najeriya cewa sojoji da sauran jami'an tsaron ƙasar nan ba za su ci amanar yan ƙasa ba a wajen ƙoƙarin su na daƙile duk wani kalan ta'adɗanci.

A wani labarin kuma Jarumar masana'antar shiya fina-finai ta Kannywood Ummy Zeezee ta roƙi mutane su saka ta a addu'a don tana cikin ƙangin rayuwa

Fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da Ummi Zeezee, ta ce ta shiga kangin rayuwa, inda har ta kan ji kamar ta kashe kanta.

A ranar Asabar, 3 ga watan Afrilu ne jarumar ta fadi hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel