Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna

Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna

- Jami'an yan sanda sun kubutar da mutanen da masu garkuwa da mutane suka sace

- Har ila yau, jihar Kaduna na fuskantar kalubale tsaro sakamakon ayyukan yan bindiga

- Gwamnan jihar ya lashi takobin cewa ba zai taba sulhu da yan bindigan ba

Gwamnatin jihar Kaduna, a ranar Asabar, ta bayyana cewa jami'an tsaro sun ceto akalla mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar.

A jawabin da kwamishanan harkokin cikin gida da tsaron jihar, Samuel Aruwan, ya saki, ya ce hukumar yan sandan jihar ce ta baiwa gwamnatin jihar rahoton ceto mutanen.

Aruwan ya yi bayanin cewa an samu nasarar ceto mutanen ne a karamar hukumar Chikun ta jihar.

Jawabin ya ce da farko, an ceto wasu mata uku a unguwar Rijiya Uku.

Jawabin yace: "A cewar rahoton, an sace wasu mata uku a ranar 18 ga Nuwamba 2020 lokacin da yan bindiga suka kai hari kauyen dake wajen jihar. Tun lokacin yan bindigan ke yawo da mutanen suna gudun jami'an tsaro har suka shigo karamar hukumar Chikun (jihar Kaduna)."

"Sakamakon labarin da aka samu ranar Alhamis 1 ga Afrilu, 2021 na cewa an gano wasu mutane, hukumar yan sanda ta tura jami'ai wajen kuma suka budewa yan ta''addan wuta, wanda ya tilastasu barin wadanda suka sace."

An ambaci sunayen wadanda aka ceto matsayin; Ladi Nuhu, Laraba Yusuf, Justina Ayuba.

KU KARANTA: Gobara ta kama babbar kasuwar kayan mota a garin Ibadan

Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna
Yan sanda sun ceto mutum 15 da akayi garkuwa da su a jihar Kaduna Credit: @KDSG
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan bindiga suk bindige shugabannin Miyetti Allah har lahira a Nasarawa

A wani harin kuwa, yan sanda sun ceto mutum 12 da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Jami'an tsaron a sintirin da suka kai sun samu mutum 12 a dajin Buruku yayinda wadanda suka sacesu suka gudu.

"Sunayensu sune Bashar Buhari, Surajo Attahiru, Hassan Adamu, Falalu Yusuf Sunusi Aminu, Shamsiya Sunusi, Adamu Sani, Suleiman Bahajetu, Salabi Mohammed, wani jariri, da wasu mazaje biyu da ba'a san sunayensu ba,” yace.

Aruwan ya ce gwamna Nasir El-Rufa'i na mika godiyarsa ga hukumar yan sandan jihar Kaduna karkashin CP Musa Muri.

An bagare guda, gwamnan Bello Matawalle na jihar Zamfara bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta ke sulhu da yan bindiga, inda yace sulhu kadai ne mafita daga matsalar tsaron jihar.

Gwamnan ya yi bayanin cewa tsakanin 2011 da 2019, yan bindiga sun hallaka mutum 2,619, sun yi garkuwa da 1,190 kuma sun karbi akalla N970 million matsayin kudin fansa daga wajen iyalan wadanda suka sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel