Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya gudana a kasar Masar

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya gudana a kasar Masar

- A jiya Asabar ne kasar Masar ta guanar da bikin nunawa duniya gawarwakin Fir'anoninta

- Kasar ta kashe makudan miliyoyi wajen gudanar daa bikin, kuma mutanen kasar sun halarta

- Mun kawo mutu hotunan yadda bikin ya gudana a kasar cikin kasaita da farin ciki

A jiya Asabar 3 ga watan Afrilu ne kasar Masar ta gudanar da wani gagarumin bikin sauyawa tsoffin Fir'aunonin kasar kaburbura zuwa wani katafaren gidan adana kayan tarihi.

An yi jerin gwanon Fir'aunonin cikin kasaita, yayin dubban dubatan mutanen kasar suka yi dafifi a yayin bikin.

An makudan miliyoyin daloli domin bikin na nuna girmamawa ga kaburburan masu dunbun tarihin da ya haura shekaru sama da 3,000, in ji Rahoton Aljazeera.

KU KARANTA: Wasu fitattun kasar nan ne ke son a raba Najeriya, talakawa babu ruwansu, Ahmad Lawan

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana
Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com
Source: UGC

An sauyawa Fir'aunonin 22 wajen zama, wadanda suka kasance 18 daga cikinsu wasu shahararrun sarakunane da kuma sarauniyoyi hudu.

Hukumomin kasar ta Masar ta rufe manyan hanyoyin da suka dangana da kogin Nilu domin nuna girmamawa ga a Fir'aunonin.

A tarihance, kasar na matukar alfahari da ajiyar sauran gawarwakin Fir'aunonin na tsawon tarihi.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda bikin ya gudana a jiya Asabar.

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana
Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com
Source: UGC

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana
Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com
Source: UGC

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana
Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com
Source: UGC

KU KARANTA: Yadda 'yan Biafra masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo

A wani labarin, Ana jerin gwanon fito da gawarwakin tsofaffin shugabannin Masar 22 da suka shude a Alkahira a yau Asabar inda za a sauya su zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi da ke kudancin birnin, BBC Hausa ta ruwaito.

Ana sa ran cincirindon jama'a za su yi jerin gwano kan tituna domin kallo - inda za su ga sarakuna 18 da sarakuna mata huɗu na Masar da za a dauka cikin akwatunan zinari.

Za a tsaurara matakan tsaro sosai, musamman daukarsu da ake a matsayin masu daraja kuma matsayin dukiyar kasar.

Source: Legit

Online view pixel