Wasu fitattun kasar nan ne ke son a raba Najeriya, talakawa babu ruwansu, Ahmad Lawan

Wasu fitattun kasar nan ne ke son a raba Najeriya, talakawa babu ruwansu, Ahmad Lawan

- Shugaban majalisar dattijai ya bayyana cewa, talakawa baburuwansu da batun raba kasa

- Shugaban ya zargi fitattun Najeriya da inziga mutane zuwa ga tunanin wargaza Najeriya

- Ya kuma sake jaddada dogewar shugaba Buhari kan tabbacin cewa Najeriya ba za ta rabu ba

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce fitattun mutane ne ke ingiza Najeriya zuwa ga wargajewa, The Cable ta ruwaito.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar, Lawan ya ce talakawa na ganin cewa ya kamata kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayin dunkulalliya da ta fi karfin ballewa.

"Na yi imanin cewa yawancin 'yan Najeriya sun yi imanin ya kamata su kasance a inuwa daya - ina nufin talakawan Najeriya," in ji Lawan a garinsu, jihar Yobe.

“Wadannan mutane ne da suka yi imani da hadin kan kasar nan. Amma fitattu nan ne inda matsalar take.

KU KARANTA: Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya

Wasu fitattun kasar nan ne ke son a raba Najeriya, talakawa babu ruwansu, Ahmad Lawan
Wasu fitattun kasar nan ne ke son a raba Najeriya, talakawa babu ruwansu, Ahmad Lawan Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

“Fitattun mutane za su gaya muku cewa, a'a, dole ne mu balle. Na yi imanin cewa ya kamata mu yi adalci ga dimbin 'yan Najeriya - musamman talakawan Najeriya."

Shugaban majalisar dattijan ya kara da cewa talakawa na son a jagorance su yadda ya kamata - kuma "dole ne mu ba su jagoranci na adalci."

Ya ce ya kamata a ko yaushe a magance korafin wadanda ke kiran ballewa amma ya kara da cewa: “Wannan ba shi ne zai zama sanannen matsayin mutane daga kowane bangare na kasar ba.”

“Don haka, na yi imanin cewa hadin kan kasar nan ba abu ne da za a tattauna ba,” in ji shi.

Sanarwar ta Lawan ta sake bayyana ra'ayin Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya dage kan cewa Najeriya ta fi karfi a dunkule maimakon a wargaje.

Kamar dai yadda kiraye-kirayen ballewa suka ta’azzara a ‘yan makwannin nan, shugaban ya ci gaba da maimaita kudurinsa na ganin cewa Najeriya ba za ta rabu ba.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta

A wani labarin, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya baiwa yan kasuwar Yan Harawa da gobara ta musu ɓanna tallafin naira miliyan N8m.

wani jawabi da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo, ya fitar, ya ce sanatan ya bada wannan gudummuwa ne ya yin da yakai ziyara kasuwar dake Gashua ƙaramar hukumar bade, jihar Yobe.

A lokacin ziyarar, Lawan ya roƙi shuwagabannin kasuwar da su tabbata dukkan yan kasuwar da abun yashafa sun sami wani abu daga cikin gudummuwar da aka baiwa kasuwar ba tare da saka siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.