Ana bikin nunawa duniya gawar Fir'auna da sauran sarakunan Masar

Ana bikin nunawa duniya gawar Fir'auna da sauran sarakunan Masar

- A yau Asabar ne ake gudanar da bikin fito da gawarwakin fir'aunoni 22 na kasar Masar

- Rahoto ya ce za a fito da sarakunan ne don nunawa duniya, tare da sauya musu wurin zama

- An bayyana cewa, za a tsaurara tsaro don tabbatar da jerin gwanon ya tafi yadda aka tsara

Ana jerin gwanon fito da gawarwakin tsofaffin shugabannin Masar 22 da suka shude a Alkahira a yau Asabar inda za a sauya su zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi da ke kudancin birnin, BBC Hausa ta ruwaito.

Ana sa ran cincirindon jama'a za su yi jerin gwano kan tituna domin kallo - inda za su ga sarakuna 18 da sarakuna mata huɗu na Masar da za a dauka cikin akwatunan zinari.

KU KARANTA: Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky

Ana bikin nunawa duniya gawar Fir'auna da sauran sarakunan Masar
Ana bikin nunawa duniya gawar Fir'auna da sauran sarakunan Masar Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Za a jera su ne daidai da tsarin tarihin mulkinsu.

Za a tsaurara matakan tsaro sosai, musamman daukarsu da ake a matsayin masu daraja kuma matsayin dukiyar kasar.

Sarakunan sun kunshi har da Sarauniya Hatshepsut ta biyar a Masar da Fir’auna da ake kira Ramses na biyu.

KU KARANTA: An kuma: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar katakon Oko Baba na jihar Legas

A wani labarin, A makon da ya gabata ne aka yi ta watsa wani bidiyo da ke nuna yadda sararin samaniyar Masallacin Ka'aba da ke kasar Saudiyya ya rikide ya zama ja jazur.

Da yawan mutane sun yi ta yada bidiyon tare da nuna yadda lamarin ya kasance, suna nuna hakan a matsayin wata alama mai nuna cewa duniya tazo karhse.

A sakon da ke yawo tare da bidiyon an ce: ... "wannan ne abin da ya faru a Saudiyya a yau, iska mai tafe da guguwar rairayin hamada mai launin ja ta rufe sararin samaniyar Masallacin Harami da kewaye."

Asali: Legit.ng

Online view pixel