Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya

Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya

- Kasar Burtaniya ta tabbatar da myuwar wasu mutane sanadiyyar allurar rigakafin Korona

- Kasashen Turai sun yi korafi a baya kan matsalar allurar rigakafin Korona ta Astra-Zeneca

- Hukumar lafiyar ta bayyana cewa, duk da haka riba da aka samu game da allurar yafi hatsarinta

Jami'iyar kula da lafiya a Burtaniya a ranar Asabar ta ce mutane bakwai cikin 30 da suka yi fama da daskarewar jini bayan sun karbi allurar rigakafin Korona ta Oxford-AstraZeneca, sun mutu.

Amincewar da Burtaniya ta yi game da mutuwar ta zo ne yayin da kasashen Turai da yawa suka dakatar da amfani da allurar ta AstraZeneca kan hadarin daskarewar jini, Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton da likitoci ko kuma jama'ar gari suka gabatar ta shafin yanar gizon gwamnati, ya zo ne bayan an yi allurai miliyan 18.1 na rigakafin a kasar.

Mafi yawan lokuta (22) sun kasance batu kan yanayin daskarewar jini wanda ake kira cerebral venous sinus thrombosis.

KU KARANTA: Ana bikin nunawa duniya gawar Fir'auna da sauran sarakunan Masar

Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya
Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya Hoto: dw.com
Asali: UGC

Majinyata takwas sun sha fama da wasu nau'ikan cututtukan thrombosis hade da kananan matakan jini, wanda ke ingiza daskarewar jini.

Babu wani rahoto game da daskarewar jini daga allurar rigakafin Pfizer-BioNTech, in ji mai kula na Burtaniya, inda ta kara da cewa "cikakken bincikenmu a cikin wadannan rahotannin yana gudana".

Amma babban jami'iyar MHRA Dr June Raine ta jaddada cewa fa'idojin da aka samu na allurar ya fi hadarin ta.

"Jama'a su ci gaba da karbar allurar rigakafin su idan aka gayyace su don yin hakan," in ji ta.

KU KARANTA: Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya tana tsara kashe Naira biliyan 396 don yin allurar rigakafin Korona a shekarar 2021 da 2022, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a ranar Laraba bayan taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Zainab ta bayyana cewa wannan adadi na iya raguwa matuka kasancewar Gwamnatin Tarayya na karbar karin gudummawar allurar rigakafin daga kamfanoni masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.