Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta

Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta

- Jam'iyyar PDP ta bayyana kudurin cire mata a biyan kudin fom na tsayawa takara a Abuja

- 'Yan takarar kananan hukumomi da kansila ne aka cire wa nauyin siyan fom a birnin

- Hakazalika jam'iyyar ta bayyana kudaden da ta saka na iyan fom din ga sauran jama'a

Kwamitin aiki na kasa (NWC) na jam'iyyar PDP ya cire dukkan 'yan takara mata a biyan kudin fom din tsayawa takara a zaben shugabannin kananan hukumomin FCT, TheCable ta ruwaito.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wani jadawalin ayyuka da Austin Akobundu, sakataren shirya taro na kasa ya fitar a ranar Asabar.

Jam’iyyar ta ce sayar da tikitin takara da fom din neman takarar shugabannin kanann hkumomi da mukaman kansila zai fara ne a ranar 6 ga Afrilu kuma zai kare a ranar 13 ga Afrilu a hedkwatar jam’iyyar na kasa.

Jam’iyyar ta tsayar da kudin fidda gwani na masu neman kujerar shugabancin kananan hukumomi akan N400,000 da N100,000 domin nuna sha'awar su.

KU KARANTA: Wasu mutum 7 sun sheka lahira bayan yi allurar rigakafin Korona a Burtaniya

Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta
Jam'iyyar PDP za ta ba matan Abuja fom din tsayawa takara kyauta Hoto: dvnews.com.ng
Asali: UGC

Ga kujerar kansila kuwa, 'yan takarar zasu biya N75,000 na fom din takara sannan N25,000 domin nuna sha'awar su.

PDP ta tsayar da N3,000 ga fom din wucin-gadi ga wakilan mazabu uku da na wakilan kasa.

Jam’iyyar ta ce ranar 14 ga Afrilu ita ce ranar karshe da za a dawo da fom da aka cike, yayin da za a tantance dukkan ‘yan takarar daga 16 ga Afrilu zuwa 17 ga Afrilu.

A cewar sanarwar, za a gudanar da taron koli na mazabu don zabar 'yan takarar kansiloli da wakilai uku a kananan hukumomi a ranar 19 ga Afrilu.

Sanarwar ta kara da cewa a ranar 22 ga Afrilu za a gudanar da taron koli na kananan hukumomi don zaben ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi.

KU KARANTA: Ana bikin nunawa duniya gawar Fir'auna da sauran sarakunan Masar

A wani labarin, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsayar da ranar 28 ga watan Yuni don ci gaba da rajistar masu jefa kuri’a gabanin zaben 2023, TheCable ta ruwaito.

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar INEC, ya sanar da ranar ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Ya zuwa shekarar 2018 lokacin da aka dakatar da rajistar, yawan masu jefa kuri’a a Najeriya ya kai miliyan 84, wanda ke nufin 40% cikin 100% na yawan mutanen kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel