Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky

Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky

- Kasar Amurka ta zargi gwamatin Najeriya da yin shuru kan lamarin kisan almajiran Zakzaky

- Amurka ta ce ya kamata ya zuwa yanzu Najeriya ta ito ta fadawa duniya halin da ake ciki

- Ana zargin sojojin Najeriya da kisan da dama daga cikin almajiran na Zakzaky a wani rikici

Wani rahoton Amurka kan batun kare hakkin dan adam a Najeriya na shekarar 2020 ya ce har yanzu babu wani karin bayani kan binciken gwamnatin tarayya ko kama wasu da ke da hannu a kashe-kashen da sojojin kasar suka yi wa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Amurka ta ce ya kamata zuwa yanzu Najeriya ta yi wani karin bayani ga duniya a kan zargin da ake yi wa dakarun sojin Najeriya na kisan almajiran Zakzaky kimanin 347, da kuma binne su a manyan kaburbura domin boye abin da aka aikata, BBC ta rahoto.

KU KARANTA: An kuma: Gobara ta yi kaca-kaca da kasuwar katakon Oko Baba na jihar Legas

Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky
Amurka na zargin Najeriya da yin rufa-rufa kan kisan almajiran Sheikh Zakzaky Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A shekarun baya ne rikici ya barke tsakanin sojojin Najeriya da almajiran Sheikh Zakzaky, lamarin da ya jawo mutuwar da dama daga cikin almajiran.

Ana zargin sojojin Najeriyan da kisan da dama daga cikin almajiran. Hakazalika aka tsare jarogaran Shi'a na Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Zakzaky na tsawon shekaru a gidan yari.

KU KARANTA: Hukumar zabe ta INEC ta sanar da ranar ci gaba da rajistar katin zabe

A wani labarin daban, Dari Bayero, babban lauyan da ke jagorantar 'shari'ar sirri' na jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya (IMN), Sheikh Ibrahim Zakzaky, da matarsa Zeenat, ya roki Babbar Kotu da ta dakatar da tuhumar ta yanke masu hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Bayero, yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan Mai Shari’a Gideon Kurada ya dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Mayu domin wadanda ake tuhumar su bude kariya kan karar, ya ce jihar ta rufe kararta bayan gabatar da shaidarta ta 15 a shari’ar.

“Daya daga cikin addu'o'inmu shi ne kotu ta yanke hukunci a kan Babu-Shari'ar-Gabatarwa, ta yi watsi da masu kariyar kuma ta hukunta wadanda ake tuhumar yadda ya dace da kuma yanke musu hukunci kamar yadda doka ta tanada,” inji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel