Kakakin kungiyar kare hakkin Yarbawa, Yinka Odumakin, ya mutu

Kakakin kungiyar kare hakkin Yarbawa, Yinka Odumakin, ya mutu

Kakakin kungiyar kare hakkin Yarabawa, Afenifere, Yinka Odumakin, ya mutu.

Odumakin ya mutu ne a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas bayan gajeruwar rashin lafiya.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Odumakin ya mutu bayan kamuwa da cutar Korona.

Matar Odumakin, Dr. Josephine Okei-Odumakin, ta bayyana cewa mijinta ya mutu ne daidai lokacin da ya fara samun lafiya.

Ta ce tun ranar 10 ga Maris yake fama da rashin lafiya.

"Tun ranar 10 ga Maris yake fama da rashin lafiya kuma yayinda ya fara samin sauki, ya fara samun matsalar numfashi," tace.

Kakakin kungiyar kare hakkin Yarbawa, Yinka Odumakin, ya mutu
Kakakin kungiyar kare hakkin Yarbawa, Yinka Odumakin, ya mutu
Source: Original

Saurari karin bayani.....

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel