Bayan ya yi allurar rigakafi: Shugaban kasar Argentina ya kamu da korona
- Shugaba Alberto Fernandez na kasar kasar Argentina a kamu da cutar korona duk da cewar an yi masa allurar rigakafin cutar
- Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter
- Sai dai ya ce yana cikin kyakyawan yanayi illa dan zanzabi da ba a rasa ba
Shugaban kasar Argentina, Alberto Fernandez, ya kamu da cutar korona duk da cewar an yi masa allurar rigakafin cutar.
An tabbatar da hakan ne bayan sakamakon gwain da aka yi masa ya fito.
Mista Fernandez, mai shekara 62, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana cikin yanayi mai kyau duk da yana fama da zazzabi.
KU KARANTA KUMA: FAAC: Jihohi 5 da suka samu kaso mafi tsoka na kudaden shiga a 2020
Sai dai kuma ya kara da cewa ya so ya gama bikin ranar haihuwarsa ba tare da samun irin wannan labarin ba.
Ga fassarar rubutun da ya wallafa a shafin nasa:
"Ina so in gaya muku cewa a ƙarshen yau, bayan kamuwa da zazzabin da ya kai 37.3 da ɗan ciwon kai, na yi gwajin korona, wanda ya tabbata ina dauke da ita.
"Kodayake muna jiran tabbaci ta hanyar gwajin PCR, amma na riga na keɓe, don yin biyayya da yarjejeniya ta yanzu da kuma bin umarnin likita na.
"Na tuntuɓi mutanen da na hadu da su a cikin awanni 48 da suka gabata don tantance ko sun yi kusa dani sosai don su kebe kansu.
"Don sanin kowa ina cikin koshin lafiya kuma, kodayake na so ace na kawo ƙarshen bikin zagayowar ranar haihuwata ba tare da wannan labarin ba, kuma ina cikin farin ciki. Ina godiya har cikin raina saboda yawan kaunar da kuka nuna min a yau, da tuna ranar haihuwata."
A watan Janairu aka yi wa Mista Fernandez rigakafin korona ta Sputnik da Rasha ta samar, shine shugaba na farko daga yankin Latin Amurka da aka yi wa rigakafin.
KU KARANTA KUMA: Hotunan amaryar da tayi biki ba tare da kwaliyya ba ya haddasa cece-kuce
A wani labarin, mun ji cewa Ubangiji ya dauki ran tsohon gwamnan jihar Delta, Rt Hon Sam Obi. Ya rasu ne da safiyar Asabar.
Har yanzu ba a riga an tabbatar da dalilin mutuwarsa ba, sai dai wata majiya mai karfi ta tabbatar da yadda aka adana gawarsa a ma'adanar gawawwaki dake Asaba.
Marigayi Sam Obi ya wakilci mazabar Ika ta arewa da gabas ta jihar Delta sau uku, tun daga 2003 zuwa 2015, sannn ya yi rikon kwaryar kujerar gwamnan jihar a 2007.
Asali: Legit.ng