Kada ku bari masu mugun nufi su raba mu, Shugaba Buhari ga yan Najeriya

Kada ku bari masu mugun nufi su raba mu, Shugaba Buhari ga yan Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya jadadda matsayinsa na cewa ’yan Najeriya sun fi kyau kuma sun fi karfi a matsayin tsintsiya madaurinki daya

- Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar da kar su bari masu barna su raba kasar

- Hakan na kunshe ne a sakonsa na bikin Ista

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya sake nanata matsayinsa cewa ’yan Najeriya sun fi kyau kuma sun fi karfi a matsayin kasa daya.

Saboda haka ya yi kira ga ‘yan kasar da kar su bari masu barna su raba kasar.

Matsayin Buhari na kunshe ne a cikin sakonsa na bikin Ista wanda aka yi wa lakabi da "Shugaba Buhari ya taya Kiristoci murnar a bikin Ista" wanda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Femi Adesina ya gabatar wa manema labarai.

Kada ku bari masu mugun nufi su raba mu, Shugaba Buhari ga yan Najeriya
Kada ku bari masu mugun nufi su raba mu, Shugaba Buhari ga yan Najeriya Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu nan: Buhari ya nada mukami daga kasar Ingila, ya rubutowa ‘Yan Majalisa takarda

Sanarwar ta ruwaito Buhari yana cewa, “Bai kamata mu kyale maganganun wasu‘ yan barna suna lalata hadin kai da galibin ‘yan kasar nan suke kauna ba.

“Kamar yadda na fada a baya, mun fi kyau kuma mun fi karfi a matsayin kasa daya a karkashin Allah.

"Ina sake taya 'yan uwanmu maza da mata murnar wannan lokaci tare da yi wa kowa barka da bikin Ista."

Shugaban kasar ya kuma ba da tabbacin cewa matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta zai zama tarihi nan ba da jimawa ba.

Ya yaba wa jami'an tsaro wadanda, in ji shi, suna ci gaba da tunkarar mutane masu muguwar dabi'a cikin tsakar dare domin kiyaye wasu.

"Na gamsu da cewa sabuwar shawarar da aka yanke tsakanin jami'an tsaro don tabbatar da cewa rashin tsaro a kasar zai zama tarihi," in ji shi.

KU KARANTA KUMA: An bayyana Shugabannin Afirka mafi tsufa a 2021 tare da hotuna da ainahin shekarunsu

Yayin da Kiristoci ke bikin Ista, Shugaban ya ce dama ce ta sabunta buri da imani, nuna kauna da jinjina ga juna ba wai yanke kauna ba, duk da kalubalen da ake ciki a wannan lokacin.

A gefe guda, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bawa yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatin ba za ta yi watsi da gajiyayyu da talakawa ba.

Shugaban kasa ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da hadimisa kan watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ranar Alhamis a yayin da kirista ke shirin bikin Easter, Channels Tv ta ruwaito.

Ya ce. "A matsayin mu na gwamnati, za mu cigaba da tabbatarwa ba mu manta da gajiyayyu, talakawa da marasa galihu a cikin mu ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng