Gwamnati Ba Za Ta Manta Da Gajiyayyu Da Talakawa Ba, Buhari Ya Tabbatarwa 'Yan Nigeria
- Shugaba Muhammad Buhari, a sakonsa na Easter ya ce gwamnatinsa ba za ta manta da talakawa da gajiyayyu ba
- Shugaban kasar ya kuma yi kira da yan kasar su zama masu kaunar juna kuma kada su cire tsammani da alheri
- Buhari ya ce gwamnatinsa ta tallafawa iyalai da masu sana'o'i domin rage radadin korona duk da karancin kudi a kasar
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bawa yan Nigeria tabbacin cewa gwamnatin ba za ta yi watsi da gajiyayyu da talakawa ba.
Shugaban kasa ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da hadimisa kan watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ranar Alhamis a yayin da kirista ke shirin bikin Easter, Channels Tv ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira
Ya ce. "A matsayin mu na gwamnati, za mu cigaba da tabbatarwa ba mu manta da gajiyayyu, talakawa da marasa galihu a cikin mu ba.
"Mun taimaka musu da tallafi duk da cewa akwai karancin kudi, mun yi iya kokarin mu wurin taimakawa iyalai da masu sana'o'i da abin ya shafa a wannan lokacin.
A yayin da kiristoci ke bikin Easter, Shugaban kasar ya ce lokaci ne na nuna kauna da godiya ga juna da fatan ganin alheri a gaba, ba cire tsammani ba duk da kallubalen da muke fuskanta.
Shugaba Buhari ya mika godiyarsa bisa sadaukarwar da likitoci da ma'aikatan jinya da sauran ma'aikatan lafiya suka yi wurin dakile yaduwar annobar korona da ceton rayyuka.
KU KARANTA: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi
Ya kuma gode wa sauran yan Nigeria saboda biyayya ga dokokin kiyayye yaduwar korona da suka hada da wanke hannu akai-akai, bada tazara, saka takunkumin fuska da yin riga-kafi.
A bangaren tsaro, Shugaban kasar ya bawa yan kasar tabbacin cewa rashin tsaro zai zama tarihi.
A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.
Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa
Asali: Legit.ng