Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana ranar da za'a kammala aikin gyaran Hanyar Abuja Zuwa Kano

Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana ranar da za'a kammala aikin gyaran Hanyar Abuja Zuwa Kano

- Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar da za'a kammala aikin gyaran hanyar data tasƙ daga Abuja ta shiga Kaduna zuwa Kano.

- Hukumomi a ma'aikatar ayyuka sun bayyana cewa ana sa ran kammala aikin a shekarar 2023

- Idan baku manta ba gwamnatin tarayya ta baiwa kamfanin Julius Berger aikin gyaran hanyar tun a watan Disamban 2017

Hukumomin ma'aikatar ayyukan ƙasar nan sun bada tabbacin lokacin da ake sa ran kammala gyaran hanyar data taso daga Abuja zuwa Kano.

Hukumonin sun ce ana sa ran kammala aikin gyaran a shekarar 2023, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan karbar N5m, yan bindigar da suka sace malami da wasu 11 sun saki gawarwaki 4

Daraktan kula da gina manyan hanya da kuma gyaran su, Mr Funso Adebiyi dake ma'aikatar ne ya bada wannan tabbacin ran Alhamis.

Adebiyi, ya bayyana haka ne ya yin da ya jagorancin wakilan ma'aikatar zuwa wurin da ake gudanar da aikin don tabbatar da yadda ake samun cigaba.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana ranar da za'a kammala aikin gyaran Hanyar Abuja Zuwa Kano
Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana ranar da za'a kammala aikin gyaran Hanyar Abuja Zuwa Kano Hoto: @Daily_trust
Asali: Twitter

A jawabin da Adebiyi ya yi yace:

"Muna tsammanin gama aikin nan daha nan zuwa ƙarshen shekarar 2023, kamar yadda mutane ke gani aikin na tafiya sosai a dukkan ɓangarorin hanyar mai tsawon kilomita 375, hanyar data taso daga Abuja ta shiga cikin Kaduna zuwa Kano."

"Mun yi matuƙar farin ciki da ingancin aikin kuma muna fatan hakan ya ɗore"

Akan aikin da aka riga akayi a hanyar, Daraktan yace an kammala sama da kilomita 100 a sashin na daya daga cikin wurare uku da ake aikin.

Sannan an kammala kilomita 40 a sashi na biyu na aikin wanda ake yi daga Kaduna zuwa zariya.

KARANTA ANAN: APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

Haka kuma an kammala kilomita 70 a sashi na uku na aikin wanda ake yi a tsakanin Zariya zuwa Kano.

Daraktan yace wasu ɓangarorin hanyar an kusa kammala su a dukkan sashi uku da aka kasa aikin.

Daga ƙarshe Adebiyi ya kira yi direbobin motoci da sauran masu amfani da hanyar da su yi tuƙi a hankali don rage hatsarin da ake yawan samu akan hanyar.

Idan zaku iya tunawa, gwamnati ta baiwa kamfanin Julius Berger aikin gyaran hanyar data taso daga Abuja ta ratsa ta cikin Kaduna zuwa Kano a watan Disamban 2017.

A wani labarin kuma Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko

Biloniyan dan siyasa, Ned Nwoko, ya ce auren mace fiye da daya yana da matukar amfani domin taimakon juna ne

A cewar dan siyasan, auren mace fiye da daya na sa a tallafi mata kuma hakan na hana su fadawa muguwar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262