Kada ku bar masu gulma da tsegumi su raba kawunanmu, Buhari ga 'yan Najeriya

Kada ku bar masu gulma da tsegumi su raba kawunanmu, Buhari ga 'yan Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari yayi kira ga 'yan kasa da su kasance masu hadin kai

- A cewar shugaban, kada jama'a su bar masu tsegumi su raba kan kasar nan har a kai ga rabuwa

- Buhari ya kara da cewa, a zaman kasar nan tsintsiya ne za a iya cimma manufofin alheri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya jaddada matsayarsa na cewa Najeriya ta fi karfi tare da tsayuwa a matsayinta na kasa daya.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, a don haka yayi kira ga 'yan kasa da kada su bar masu bata musu suna su raba kasar nan.

Matsayar Buhari na kunshe ne a sakon ista wanda shugaban kasan ya taya 'yan Najeriya mabiya addinin Kirista murnar bikin, wanda Femi Adesina ya mika ga manema labarai.

KU KARANTA: Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

Kada ku bar maɓarnata su raba mu, Buhari ga 'yan Najeriya
Kada ku bar maɓarnata su raba mu, Buhari ga 'yan Najeriya. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Mun damke masu daukar nauyin ta'addanci, lamarin zai firgita jama'a, Fadar shugaban kasa

Kamar yadda takardar ta sanar, "Kada mu bar masu bata suna sun yada zantuka marasa dadi domin kawo rabuwar kai ga 'yan kasa.

"Kamar yadda nace, mun fi zama tsayayyu kuma masu karfi a matsayinmu na kasa daya karkashin ikon Ubangiji.

“Ina taya 'yan uwana maza da mata murnar Ista da kuma fatan za a yi bikinta lafiya."

Shugaban kasan ya kara da bada tabbacin cewa kalubalen tsaron da ke addabar kasar nan zai zama tarihi wata rana.

Ya jinjinawa jami'an tsaro wanda ke cigaba da fuskantar miyagun mutane a cikin dare mai duhu duk don bada kariya ga al'umma.

"Na sakankance cewa sabon salon tsaro na kasar nan zai sa kalubalen tsaro ya zama tarihi nan babu dadewa," yace.

A wani labari na daban, Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya yi allurar riga-kafin cutar korona ta AstraZeneca.

A watan Afirilun 2020, tsohon ministan ya kwatanta riga-kafin cutar corona da muguntar da za ta yi sakamakon mutuwar mililoyin jama'a.

A watan Mayun 2020, yayin da ake ta cigaba da samar da riga-kafin cutar, tsohon ministan sufurin jiragen saman ya kushe wannan cigaba a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa an mayar da mutane "aladun turawa".

Asali: Legit.ng

Online view pixel