Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

- Tsohon shakikin abokin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Buba Galadima, yace kan 'yan APC a rabe yake

- Dan jam'iyyar PDP yace a halin yanzu APC ta kasu zuwa kungiyoyi uku kuma kowacce kungiya na so ta fitar da dan takara

- Galadima yace Allah ne ya kama su kuma zai tarwatsa su, amma da kansu a hade yake, babu shakka akwai wuya kwace mulki a hannunsu

Buba Galadima, tsohon makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce akwai banbance-banbance a APC wadanda ba za a iya sasantasu.

Galadima ya sanar da hakan ne yayin wani shirin gidan talabijin na AIT a ranar Laraba.

Ya yi magana a kan yuwuwar jam'iyyar mai mulki ta tsayar da hakalinta kan dan takara daya a zaben shugaban kasa na 2023 dake tahowa.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, Galadima yace 'yan jam'iyyar APC sun rarrabe kansu zuwa kungiyoyin da sai dan kungiyar za su goyi bayan ya zama shugaban kasa a 2023.

KU KARANTA: Matar Aure Tayi wa Ɗan Kishiya Mugun Duka, ya Sheƙa Lahira

Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023
Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaban CCT ya suburbudi maigadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'

Ya ce 'yan jam'iyyar hudu, biyu daga kudu, biyu daga arewa, sun dauka alwashin goyon baya.

"Jam'iyyar APC ta rabu zuwa kungiyoyi uku, a takaice kungiyoyi uku da rabi. Bakwai, bakwai, gwamnoni biyar. Kowacce kungiyar dan kungiyarta kadai za ta goyi baya ya tsaya a matsayin dan takarar shugaban kasa," yace.

“Toh muna dai kallonsu. Allah ne ke kama su daya bayan daya. Saboda idan da Allah ya barsu a tare, akwai matukar wuya a kwace gwamnati daga hannunsu. Hakan ne yasa suke ta janyo jama'a tare da nisantar tsoffin magoya bayansu."

A wani labari na daban, Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce kasar nan na fuskantar zaman lafiya duk da irin kalubelen tsaro da take ciki.

Rundunar sojin kasar nan sun kasance suna yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabas sama da shekaru 10.

The Cable ta ruwaito cewa, dakarun suna cigaba da gwagwarmaya da 'yan bindigan da suka addabi yankin arewa maso yamma da sauran sassan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel