Duk da kiran allurar riga-kafin korona da 'mugunta', Fani-Kayode ya je an yi mishi
- Tsohon minsitan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya karba allurar riga-kafin korona
- Duk da caccakarta da ya dinga yi, yace bayani da kuma dabaru mafifita ne suka sa ya tsaya aka yi masa
- A kwanakin baya, Fani-Kayode ya kira riga-kafin da 'mugunta' da kuma yunkurin mayar da jama'a aladun Turawa
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya yi allurar riga-kafin cutar korona ta AstraZeneca.
A watan Afirilun 2020, tsohon ministan ya kwatanta riga-kafin cutar corona da muguntar da za ta yi sakamakon mutuwar mililoyin jama'a.
KU KARANTA: Boko Haram da 'yan bindiga: Ministan Buhari yace an samu zaman lafiya a Najeriya
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun sheke 'yan Boko Haram dake dasa bama-bamai a Borno
A watan Mayun 2020, yayin da ake ta cigaba da samar da riga-kafin cutar, tsohon ministan sufurin jiragen saman ya kushe wannan cigaba a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa an mayar da mutane "aladun turawa".
Amma a ranar Talata, Fani-Kayode, yayin karbar allurar, yace dole ce ta sa ya rissinawa tunani mafi fifiko da kuma dabara.
"Ina mika godiya ga 'yar uwata, Sanata Grace Bent, wacce ta iya shawo kaina na karba allurar kuma tace dole ne mu zama abun koyi da misali ga wasu," ya wallafa.
Tsohon ministan ya kara da cewa idan har tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump zai iya yin riga-kafin duk da caccakarta da tambayoyi da yayi, toh tabbas zai iya yi.
Tunda Najeriya ta karba riga-kafin, fitattun 'yan Najeriya da suka hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun yi riga-kafin a bainar jama'a.
A wani labari na daban, mayakan ta'addancin na Boko Haram shida, fararen hula uku da wani sojan kasar Kamaru sun mutu a ranar Asabar, 27 ga watan Maris, a harin daren da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai sansanin sojoji dake Dabanga, yankin arewacin Kamaru.
Kamar yadda ganau ya sanar, mayakan dauke da miyagun makamai sun isa sansanin a motoci da babura yayin da suka ga dare ya fara yi.
"Sun wuce bayan mun dawo daga Masallaci. A zatonmu dakarun soji ne dake aikin sintirin da suka saba," Adamou Adoum, daya daga cikin 'yan sa kan yankin ya sanar.
Asali: Legit.ng