Boko Haram: Mun damke masu daukar nauyin ta'addanci, lamarin zai firgita jama'a, Fadar shugaban kasa
- Fadar shugaban kasa tace ta kama wasu wadanda ke da hannu a daukar nauyin ta'addancin Boko Haram
- Garba Shehu ya bayyana cewa za a fallasa bayanai a kan kamen da aka yi bayan kammala bincike kan lamarin
- Kamar yadda hadimin shugaban kasan ya sanar, ana zuwa har wuraren bauta domin halaka jami'an tsaro
Gwamnatin tarayya ta ce jami'an tsaro sun damke wasu 'yan Najeriya dake daukar nauyin ta'addancin Boko Haram.
Babban mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Talata, 30 ga watan Maris yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin na Channels.
Legit.ng ta tattaro cewa, Shehu yace jama'a za su matukar girgiza idan suka ji bayanin binciken da ake kan makuden kudin da ake turawa kungiyar.
KU KARANTA: Kudaden fansa ake amfani dasu wurin cigaban Boko Haram, Gwamnoni
KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai farmaki sansanin soji, mutum 9 sun sheka lahira a Dabanga
Ya ce wadanda aka kama sun hada da 'yan canji dake zama a kasashen ketare.
Shehu yace: "Yan canji ne ke turawa 'yan ta'adda kudi. Mun riga mun yi aiki da UAE. Mun damke 'yan Najeriya dake turawa 'yan ta'addan Boko Haram kudi kuma lamarin yana faruwa har a cikin gida. Kuma ina sanar daku cewa idan mun gama bincike, sakamakon zai gigita 'yan Najeriya."
Ya kara da cewa, 'yan ta'adda na kai farmaki wuraren bauta inda suke halaka jami'an tsaro, ya tabbatar da cewa jami'an bincike na sirri suna aiki a kan hakan.
A wani labari na daban, Ibrahim Attahiru, shugaban rundunar sojin Najeriya ya tabbatar da cewa rundunar za ta zama gawurtacciya da za ta dinga shawo kan kalubalen tsaro a kasar nan.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya sanar da hakan ne yayin taron watanni uku na farkon shekara na rundunar da aka yi a ranar Litinin a Abuja.
A wata takarda da Mohammed Yerima, kakakin rundunar yasa hannun, Attahiru yace sabon salon tsaron da za su mayar da hankali shine gyaran rundunar ta kowanne fanni a kasar nan ta yadda za su iya tunkarar kowanne kalubale.
Asali: Legit.ng