Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

- Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno da tawagarsa sun taimakawa mata masu itace

- Wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta sun nuna gwamnan sanye da farin jamfa da babban riga ya tsaya a titi da tawagarsa

- Hotunan sun nuna an loda itacen a daya daga cikin motocin da ke ayarin gwamnan da nufin taimakawa matan

An gano gwamna jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a baya bayan nan ya tsaya tare da ayarin motocinsa ya taimakawa wasu mata da 'yan mata da ke diban itace a gefen titi.

A wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta, an gano gwamnan kewaye da hadimansa suna taimakawa wasu mata.

Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji
Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji
Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji. @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Lakaɗawa Duka Har Suka Zubarwa Wani Haƙoransa

Babu tabbas game da ranar da abin ya faru ko kuma wurin da ya faru amma hotunan sun dauki hankulan mutane da dama a dandalin sada zumunta.

Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji
Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji
Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Duba da cewa abin da gwamnan ya yi ba lamari bane da ya fiye faruwa, mutane da dama sun ta yaba wa gwamnan kan tausayi da sanin ya kamata da ya nuna, yayin da wasu kuma ke ganin siyasa ce kawai.

Hotunan sun nuna hadiman gwamnan sun loda itacen a bayan mota mai kama da Hilux da nufin taimakawa matan daukar kayan itacen da suka samo daga daji.

KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Daba Sun Kaiwa Hadimin Ministan Buhari Da Wasu Ƴan Majalisa Hari a Osun

Jihar Borno na cikin jihohin arewa maso gabas da har yanzu yan ta'adda su kan kai hare-hare a wasu sassan jihar duk da cewa a yan kwanakin nan rundunar sojin Nigeria ta sanar da cewa ta yi nasarar kashe yan Boko Haram 48 tare da ceto mutane 11.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel