'Yan sanda sun damke wadanda ake zargi da kaiwa Soludo hari

'Yan sanda sun damke wadanda ake zargi da kaiwa Soludo hari

- Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta damke daya daga cikin wadanda ake zargi da kaiwa Charles Soludo hari

- Gungun 'yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya wuta inda suka kashe 'yan sanda

- Lamarin ya faru ne yayin da dan takarar kujerar gwamnan jihar Anambra yaje ganawa da masu ruwa da tsaki da 'yan siyasa

'Yan sanda sun damke wani da ake zargin yana da alaka da harin da aka kaiwa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Charles Soludo, a jihar Anambra.

Channels TV ta ruwaito cewa, Ikenga Tochukwum, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

Farfesa Soludo, wanda shine yake son fitowa takarar kujerar gwamnan jihar Anambra, ya halarci taron masu ruwa da tsaki da wasu 'yan siyasa a karamar hukumar Aguata dake jihar.

KU KARANTA: Kan 'ya'yan jam'iyyar APC a rarrabe yake, Buba Galadima yayi magana kan zaben 2023

'Yan sanda sun damke wadanda ake zargi da kaiwa Soludo hari
'Yan sanda sun damke wadanda ake zargi da kaiwa Soludo hari. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

KU KARANTA: Shugaban CCT ya suburbudi maigadi a Abuja, ya ce yayi masa 'tsageranci'

Yayin da ake taron a yammacin ranar Laraba, gungun ''yan bindiga sun kai hari tare da yin musayar wuta da jami'an tsaro.

A sakamakon haka, miyagun sun yi garkuwa da kwamishinan hulda da jama'a na jihar, Emeka Ezenwanne.

Bayan aukuwar lamarin, kwamishinan 'yan sanda na jihar Anambra, Monday Kuryas, ya jagoranci jami'ai zuwa inda lamarin ya faru domin dubawa.

Tochukwum yace jami'ai uku ne suka samu rauni sakamakon harbin bindiga yayin arangama da miyagun.

Ya kara da cewa, daga bisani an gano jami'an tsaron sun rasu a asibiti kuma an adana gawawwakinsu.

Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa Kuryas da sauran 'yan sandan sun ziyarci Farfesa Soludo domin kara tabbatar da tsaro a gidansa da kuma yankin Isuofia.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce jami'an tsaro sun damke wasu 'yan Najeriya dake daukar nauyin ta'addancin Boko Haram.

Babban mai baiwa shugaban kasa shawara a harkar yada labarai, Garba Shehu, ya sanar da hakan a ranar Talata, 30 ga watan Maris yayin da ya bayyana a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin na Channels.

Legit.ng ta tattaro cewa, Shehu yace jama'a za su matukar girgiza idan suka ji bayanin binciken da ake kan makuden kudin da ake turawa kungiyar.

Source: Legit.ng

Online view pixel