Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gwangwaje Ɗaliban jihar da tallafin karatu

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gwangwaje Ɗaliban jihar da tallafin karatu

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya mince a fidda kuɗi kimanin 400 miliyan don ba ɗaliban jihar tallafin karatu na zangon 2020/2021

- Hakanan gwamnan ya amince da fitar da kuɗaɗe don biyan ɗalibai yan asalin jihar dake karatu a wasu kasashen waje.

- Ya kuma bada umarnin fara tantance ɗalibai yan asalin jihar nan take don fara biyansu haƙƙoƙin su

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da fitar da kuɗi naira 400 miliyan don biyan ɗalibai yan asalin jihar tallafin karatu na zango 2020/201.

Tallafin ya shafi ɗalibai yan asalin jihar ta Zamfara dake karatu a cikin jihar da ma waɗanda ke karatu a wasu makarantun ƙasar nan.

KARANTA ANAN: APC a Ingila: Kanzon kuregene, ba a yi zanga-zangar adawa da Buhari a kasar Landan ba

Wannan na daga cikin wani jawabi ɗauke da sa hannun Yusuf Idris, Daraktan yaɗa labaran gwamnan, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Ya ce ƙarkashin zangon karatu na 2020/2021, gwamnan ya amince a fitar da 186.6 miliyan don biyan ɗaliban likitanci yan asalin jihar da a yanzun suka shiga shekara ta biyu a karatunsu a ƙasar Sudan.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gwangwaje Ɗaliban jihar da tallafin karatu
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gwangwaje Ɗaliban jihar da tallafin karatu Hoto: @Zamfara_state
Asali: Twitter

Hakanan kuma Matawalle ya amince a fidda kuɗi 24.5 miliyan don biyan ɗalibai 25 da gwamnatin ke ɗaukar nauyi a ƙasar India.

Kuma ya amince da fitar da 56.4 miliyan ga ɗaliɓan dake karatu a Cypros.

KARANTA ANAN: Auren mace fiye da daya yana habaka tattalin arziki, Biloniya Ned Nwoko

A cewar daraktan yaɗa labaran gwamnan: "Bayan gano gaskiyar lamarin bashin da ɗaliban jihar ke bin gwamnati na tallafinsu a jami'ar Al-hikmah Ilorin, jihar Kwara da jami'ar Crescent dake Abeoukuta, jihar Ogun, gwamnan ya bada umarnin fitar da 70 miliyan."

Gwamnan ya kuma amince da biyan 19 miliyan ga ɗaliban dake karatun lauya na zangon karatun da ya gabata, 2019/2020.

Ya ƙara da cewa gwamna Matawalle ya bada umarnin fara tantance ɗalibai yan asalin jihar dake karatu a makarantun gaba da sakandire a sassa daban-daban na ƙasar nan.

A wani labarin Gwamnan PDP ya yi wa Shugaba Buhari shakiyanci a kan zuwa kasar Ingila ganin Likitoci

Mai girma gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya na cewa ba zai bar Najeriya, ya yi tafiya zuwa waje saboda duba lafiyarsa ba.

Yayin da ya hadu da wata kungiyar likitoci da malaman hakori a gidan gwamnatin Ribas, Nyesom Wike ya ce babu abin da zai kai shi kasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262