Gwamnan PDP ya yi wa Shugaba Buhari shakiyanci a kan zuwa kasar Ingila ganin Likitoci
- Nyesom Wike ba ya goyon a kashe kudi wajen zuwa asibiti a kasar waje
- Gwamnan na Ribas ya ce ya tanadi duk abin da ake bukata a jihar Ribas
- Wike ya ce ya shafe sama da shekaru biyu bai yi tafiya zuwa ketare ba
Daily Trust ta rahoto Mai girma gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya na cewa ba zai bar Najeriya, ya yi tafiya zuwa waje saboda duba lafiyarsa ba.
Yayin da ya hadu da wata kungiyar likitoci da malaman hakori a gidan gwamnatin Ribas, Nyesom Wike ya ce babu abin da zai kai shi kasar waje.
Gwamna Nyesom Wike ya ke cewa duk abin da yake bukata na kula da lafiyarsa, ya na cikin asibitin gidan gwamnati da yake zaune a ciki a Fatakwal.
KU KARANTA: Buhari zai tafi Ingila ganin Likita - Fadar Shugaban kasa
Gwamna Wike yake cewa: “Halin da asibitoci su ke ciki a Najeriya ya na bukatar matukar kula sosai. Halin da mu ka samu kanmu a yau abin takaici ne.
Ya ce: “Ba na so in yi magana game da wadanda su ke yin tafiya domin a duba lafiyarsu. Sama da shekaru biyu kenan, ban yi tafiya zuwa wani wuri ba.”
“Idan mu na da duka wadannan kayan aiki a nan, me zai sa mu tafi ketare? Mu na da duk abubuwan da ake bukata domin samar da wadannan kayan.”
"Me zai kai ni zuwa kasar waje a duba lafiya ta bayan ina da duk wasu kaya a gidan gwamnati?"
KU KARANTA: Buhari ya shiga bankado sirrin ‘Yan garkuwa da mutane da Boko Haram
Ba na bukata. Duk abin da ake nema domin ayi mani wani gwaji ya na nan. Mu na da dukiya. Me zai hana mu yi wa mutanenmu aiki da ita?” inji sa.
Wike yake cewa zuwa asibitin kasar waje zai ci makudan kudi, don haka ya ce ya na da muhimmanci a kashe kudi a gyara asibitocin gida.
Gwamnan ya yi wannan magana ne a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Ingila domin ya ga likitoci kamar yadda ya saba.
Tafiyar shugaban Najeriyar ta jawo surutu, inda ‘yan kasa su ke zargin shi da batar da kudin jama’a a ketare, maimakon a gyara asibitocin Najeriya.
Irinsu Dino Malaye su na ganin ya kamata shugaban kasar ya mika mulki ga mataimakinsa.
Asali: Legit.ng