Ku Taimaka kada ku shiga yajin aiki, Gwamnatin tarayya ta Roƙi Likitocin Ƙasar nan

Ku Taimaka kada ku shiga yajin aiki, Gwamnatin tarayya ta Roƙi Likitocin Ƙasar nan

- Gwamnatin tarayya ta roƙi ƙungiyar likitocin ƙasar nan da su yi wa Allah kada su shiga yajin aikin da suke shirin yi

- Ministan ƙwadugo, Chris Ngige ne ya yi wannan kiran yana mai cewa rayuwar yan Najeriya musamman majinyata zata shiga wani hali

- Ya ce Najeriya na cikin wani mawuyacin hali saboda annobar Korona saboda haka yakamata likitocin su sake dubawa.

Gwamnatin tarayya ta faɗawa ƙungiyar likitocin cikin gida (NARD) cewa su duba halin da 80% na yan najeriya dake bukatar kulawa da lafiyar su ka iya shiga idan suka tsunduma yajin aiki.

KARANTA ANAN: NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

Ministan ƙwadugo, Chris Ngige, yace ƙasar na cikin wani mawuyacin hali a ɓangaren lafiya saboda annobar COVID19 da ake fama da ita.

A wani taro da suka yi da shuwagabannin ƙungiyar NARD a Abuja, Ngige yace mafi yawancin buƙatun likitocin na gab da cikawa tun kafin su turo wasiƙar ƙorafi da kuma sanarwar shiga yajin aiki.

Kafin su shiga taron, Ngige ya bayyana cewa gwamnati ta fara tattaunawa kan kuɗaɗen ma'aikatan lafiya na ƙasar, jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Ya ce: "Mun zo nan ne saboda mun fara warware matsalolinku, mun ɗauki matakai kuma munsa musu wa'adin cika su. Mun zo nan ne mu tattauna kan waɗannan matakan kuma musa musu lokacin da ya kamata, don hakan zai ba jami'an gwamnati damar da zasu aiwatar da su."

Ku Taimaka kada ku shiga yajin aiki, Gwamnatin tarayya ta Roƙi Likitocin Ƙasar nan
Ku Taimaka kada ku shiga yajin aiki, Gwamnatin tarayya ta Roƙi Likitocin Ƙasar nan Hoto: @SenChrisNgige
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa tsohon gwamnan CBN wuta, sun kashe mutum 3

Ministan yace sun tattauna da ma'aikatar kuɗi, kuma sun faɗa mishi cewa sun fara warware matsalolin ma'aikatan lafiya.

Haka nan kuma kwamitocin majalisar tarayya suna ƙoƙarin ganin an biya ma'aikatan lafiya haƙƙoƙinsu.

Chris Ngige ya ƙara da cewa:

"Mun shigo lamarin ne don tabbatar da anyi abinda yakamata a fannin lafiya. Muna cikin wani mawuyacin hali a fannin lafiya na duniya baki ɗaya, Najeriya tana ciki ita ma, sabida haka dole mu duba halin da yan Najeriya ke ciki."

"A halin yanzu, 80% na Yan Nageriya majinyata ne saboda annobar korona. Saboda haka dole mu kalli lamarin ta nan ɓangaren muga taya zamu ɓullo wajen warware matsalolin."

Sakataren ma'aikatar lafiya, Abdullahi Mashi, ya roƙi likitocin da su sake duba maganar shiga yajin aikin nan.

A ɓangaren sa shugaban NARD yace ƙungiyarsu a shirye take taga an warware komai a wannan taron nasu.

A wani labarin kuma 'Yan Najeriya sun yi wa Buhari zanga zanga a hanyar shiga gidansa na Landan

Sun yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya koma kasarsa yayin da suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington da ke birnin Landan.

-Hakan na daga cikin adawa da suke yi da tafiyar Buhari Birtaniya domin a duba lafiyarsa yayinda kasar ke cikin wani yanayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel