Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhurriyar Nijar

Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhurriyar Nijar

- Shugaba Buhari ya yi tsokaci kan kokarin juyin mulki a jamhurriyar Nijar

- Buhari ya yi magana da shugaban kasar Nijar a waya don jajanta masa

- Buhari ya yi kira ga Sojoji su girmama zabin da jama'a suka yi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhuriyyar Nijar.

Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana alhinin shugaban a jawabin da ya saki da yammacin Laraba.

Buhari yace "ba zai yiwu wasu su yi kokarin tunbuke gwamnatin da jama'a suka zaba ba a dukkan kasashen duniya."

Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari ya yi magana da takwararsa na Nijar, Mahamadou Issoufou, kan abinda ya faru ta wayar tarho.

"Jahilci ne ayi kokarin tunbuke gwamnatin demokradiyya da karfin Soja," Buhari yace.

"Ya kamata Sojoji sun girmama zabin al'umma kuma su girmama kundin tsarin mulki."

Shehu ya kara da cewa Buhari ya yi amfani da daman wajen taya zababben shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, murnar nasarar da yayi a zabe.

KU KARANTA: Hadimin Buhari ya fara fallasa masu daurewa Boko Haram da Miyagun ‘Yan bindiga gindi

Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhurriyar Nijar
Buhari ya yi Alla-wadai da yunkurin juyin mulki a jamhurriyar Nijar Credit: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayinda yan sanda suka fatattaki gungun yan shi'a a Abuja

Kun ji an yi yunkurin juyin mulki a Jumhuriyar Nijar, sai dai kuma ba a cimma nasarar hakan ba.

Shashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga a kusa da fadar Shugaban kasar da ke birnin Yamai.

An kuma tattaro cewa wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje dake birnin na Yamai sun yi kira ga ma'aikatansu da su zauna a gida.

Rahotanni sun kawo cewa an damke wasu sojoji a Jamhuriyar Nijar bayan sun yi yunkurin tunkudar da zababbiyar gwamnatin kasar ta hanyar yin juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel