Abun farin ciki: Ma’aurata na shirin tarban dansu na fari bayan shekaru 25 da aure
- Wasu ma'aurata 'yan Najeriya sun kwashe shekaru 25 suna jiran Allah ya azurtasu da haihuwar ‘ya’ya
- Wata mai amfani da Facebook mai suna Ujiro Isibeluo Erighono ta bayyana cewa a karshe Allah ya amsa addu’o’insu
- Ujiro ta wallafa kyawawan hotunan matar wacce ke dauke da juna biyu da mijinta don karfafawa ma'auratan da basu samu haihuwa ba gwiwa
Wasu ma'aurata yan Najeriya na shirin tarbar dansu na fari bayan shekaru 25 da aure.
Wata mai amfani da shafin Facebook da aka ambata da suna Ujiro Isibeluo Erighono ce ta yada wannan labari mai dadi, inda a yanzu ta goge sakon.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makami a Kaduna
A cewar Yabaleft, Ujiro ta rubuta a shafinta:
"Kyakkyawan OMAM, don Allah ku taya ni gode ma Allah madaukaki Wanda ya sa hakan ya yiwu.
"Wannan babbar ‘yayar tawa ta jira kuma ta yi imani da Allah tsawon shekaru 25. Amma a yau, Allah ya ba ta sabon suna o. Allah mai aminci ne koyaushe.
"Wannan godiya don ƙarfafawa wani gwiwa ne. Kawai ka zamo mai imani sannan ka amince da Shi. Idan ba ka san zafin ba, ba za ka fahimci yabon ba. Godiya ta tabbata ga Allah har abada."
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An yi yunkurin juyin mulki a Nijar, amma ba a yi nasara ba
A wani labarin, wata 'yar Najeriya da ke amfani da shafin Twitter @Raahmatuallah ta yi farin ciki kan manhajar bayan ta yi aure da burin ranta.
A wani wallafa da tayi a ranar Asabar, 27 ga Maris, matar wacce ke cike da farin ciki ta bayyana cewa sun yi aure ne bayan sun hadu da junansu a Twitter na tsawon watanni 8.
Matashiyar ta wallafa hotunan bikin nasu tare da mijinta a sanye da kayan sojoji. An yi mata kwaliyya sanye da farin kayan amare.
Asali: Legit.ng