Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriyar Burtaniya

Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriyar Burtaniya

- Sowore ya bukaci 'yan Najeriya mazauna Landan da su mamaye asibitin da Buhari zai ziyarta

- Sowore ya bayyana hakan biyo bayan sanar da cewa shugaban kasar zai tafi Landan duba lafiyarsa

- Ya siffanta tafiyar shugaban kasar da almubazzaranci da kudin kasa ba gaira ba dalili

Wani mai rajin kare hakkin dan adam kuma mawallafin jaridar SaharaReporters, Omoyele Sowore, ya shawarci ‘yan Nijeriya da ke Ingila su mamaye asibitin Landan inda Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ke shirin zuwa don duba lafiyarsa.

Sowore ya bayyana tafiyar shugaban zuwa Landan a matsayin barnatar da dukiya, yana mai cewa ya kamata Shugaban kasa ya duba lafiyarsa a asibitin "mai daraja ta duniya" da ya gina tun hawan sa mulki.

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya mazauna Burtaniya da su mamaye Abuja House da ke Landan inda shugaban zai zauna.

KU KARANTA: Ta ya zai yiwu: Shenu Sani ya caccaki batun Tinubu na daukar sojoji miliyan 50

Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriya Burtaniya
Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriya Burtaniya Hoto: techcrunch.com
Asali: UGC

"Yan Najeriya mazauna Burtaniya dole ne su #mamaye asibitin da mara lafiya @mbuhari ke barnatar da dukiyar Najeriya da ofishin jakadancin Najeriya da kuma Abuja House a Landan.

"Ya kamata Buhari ya dawo gida a duba lafiyarsa a asibiti "mai daraja ta duniya" da ya gina tun zuwansa karagar mulki. #Buharimustgo!” ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Labarin tafiyar shugaban kasar na neman lafiya ya zo ne a dai-dai lokacin da Kungiyar Likitocin Najeriya a ranar Litinin suka dage kan shiga yajin aiki a duk fadin kasar a ranar Alhamis.

Kungiyar ta kafa matsaya a kan abin da ta bayyana a matsayin rashin gaskiyar Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyoyi.

KU KARANTA: Jihar Kano ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, in ji Tinubu

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi daga tashar jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja domin zuwa kasar Birtaniya.

Hadimin Buhari kan gidajen talabijin da rediyo, Buhari Sallau, ya bayyana hakan da misalin karfe 3 na rana.

A cewarsa, Buhari zai gana da Likitansa don duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.