Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayinda yan sanda suka fatattaki gungun yan shi'a a Abuja

Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayinda yan sanda suka fatattaki gungun yan shi'a a Abuja

- Rundunar yan sanda ta tarwatsa wasu gungun yan shi'a a babban birnin tarayya Abuja, ya yin da suke zanga-zanga.

- Mutum ɗaya mai suna Muhsin Abdalla ya rasa ran sa a ya yin da wasu da dama suka jikkata harda jami'an yan sanda

- mambobin IMN din sun ce suna zanga-zanga ne don neman a sako musu jagoran su, Ibrahim Zakzaky da gwamnati ta kama

Ɗaya daga ciki yan ƙungiyar shi'a (IMN) ya mutu a ya yin da jami'an yan sandan Abuja ke ƙoƙarin tarwatsa gungun mambobin ƙungiyar dake zanga-zanga a babban birnin tarayya.

KARANTA ANAN: Ba zan taba goyon bayan tsawaita mulki ga Shugaba Buhari ba - Lawan

Sai dai har yanzin rundunar yan sandan birnin tarayya, Abuja, basu ce komai game da lamarin ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Duk da cewa rahoton ya bayyana cewa wani harsashi ne da ba shi aka nufa dashi ba ya kashe shi kuma wasu da yawa sun jikkata.

Mai magana da yawun IMN, Ibrahim Musa ya yi zargin cewa "Yan sandan sun buɗe ma mutanen mu yan shi'a wuta, suka kashe Muhsin Abdalla sannan suka jikkata wasu da dama."

Mambobin ƙungiyar ta Shi'a, IMN, suna zanga-zangar neman a saki jagoransu, Ibrahim Zakzaky, da matar sa a lokacin da lamarin ya faru.

Mutum ɗaya ya rasa ransa, Ya yin da Rundunar yan sanda suka fatattaki gungun yan shi'a a Abuja
Mutum ɗaya ya rasa ransa, Ya yin da Rundunar yan sanda suka fatattaki gungun yan shi'a a Abuja Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

Sai dai Yan sandan Abuja sun bayyana cewa sun tarwatsa yan ƙungiyar IMN ɗin ne bayan sun fara ƙoƙarin tada hargitsi a Unguwar Maitama dake Abuja.

KARANTA ANAN: Babban abin da ya sa aka shirya Maulidin Tinubu a jihar Kano – Jigon Kwankwasiyya

Yan sandan ta bakin mai magana da yawun su, Mariam Yusuf, ta ce wasu daga cikin yan ƙungiyar sun fara lalata abubuwa da kuma kai farmaki ga waɗanda basu ji ba basu gani ba harda jami'an yan sanda.

Mambobin na IMN sun fara jifan mutane da jami'an mu ta hanyar amfani da duwatsu da kuma wasu abubuwa masu hatsari.

Ta ƙara da cewa Saboda hakan da suka yi, shine yasa rundunar yan sanda taga baza ta iya barin ana lalata kayayyaki ba kuma ana jifan jami'anta.

Yan sandan sun kuma bayyana hotunan jami'ansu da aka jiwa rauni da kuma motar sintiri da aka lalata.

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun cafke wani mai sana'ar kafinta a Abuja Saboda ya Zargi Tsohon Minista

Rundunar yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani mai san'ar kafinta da zargin yana bata ma tsohon minista suna.

Kafintan dai yace shi ba bata masa suna yake ba yana neman a biyashi haƙƙinsa ne kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel