Babban abin da ya sa aka shirya Maulidin Tinubu a jihar Kano – Jigon Kwankwasiyya

Babban abin da ya sa aka shirya Maulidin Tinubu a jihar Kano – Jigon Kwankwasiyya

- Aminu Abdussalam Gwarzo ya soki taron Bola Tinubu da aka yi a Kano

- Jagoran na Kwankwasiyya da PDP ya ce gangar 2023 ne Tinubu ya buga

- Gwarzo ya na ganin babu abin da ya hada taron da yunkurin hadin-kai

Daya daga cikin kusoshin PDP na bangaren Kwankwasiyya a jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi magana kan bikin Bola Tinubu da aka shirya.

Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce siyasa ce kurum ta sa aka zabi ayi bikin taya Asiwaju Bola Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa a jihar Kano.

Tsohon kwamishinan yake cewa ta bayyana cewa an zabi ayi bikin a Kano ne saboda manufar siyasa. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a dazu.

KU KARANTA: Tinubu ya nemi tafinta ya rika fassara masa Hausa - Shehu Sani

Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya yi takarar mataimakin gwamnan Kano a karkashin PDP a 2019 ya ce ba wai don kishin-kasa aka yi taron bana a Kano ba.

Jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya ce ba ayi bikin bana a Legas kamar yadda aka saba ba ne saboda kokarin jawo hadin-kai da kaunar juna a Najeriya.

A cewar Aminu Abdussalam Gwarzo, Bola Tinubu ya samu damammakin da zai nuna cewa shi shugaban kowa ne, amma bai yi amfani da damar da ya samu ba.

“Babu abin da ya hada (biki a Kano) da hadin-kai da zaman lafiya. A lokacin da aka bukaci mutane su tashi a kirga su, ba ya nan.” Inji jagoran jam’iyyar adawar.

Babban abin da ya sa aka shirya Maulidin Tinubu a jihar Kano – Jigon Kwankwasiyya
Aminu Abdussalam Gwarzo da Bola Tinubu
Source: UGC

KU KARANTA: Bola Tinubu ya yaba wa Ganduje, ya ce Kano ta fi ko ina zaman lafiya

“Abubuwa da yawa sun faru kwanan nan, na baya shi ne mummunan ta’adin da aka yi a Shasha, a matsayinsa a APC, ya kamata ya yi kokarin ganin rikicin ya lafa.”

“A matsayinsa na mai burin mulkin kasar nan, ya kamata Tinubu ya mike ya yi magana mai kyau. Ba za ka zo kawai ka yi magana a nan ba, ka ce na hada-kai.”

"A iyaka tunanina, lissafin siyasa ce, 2023 ake hari. Gwamnatin APC ta gaza, babu abin da Tinubu zai fada, ana rasa rayuka kullum, ba a kudu maso yamma kawai ba.”

Dazu kun ji cewa Bola Tinubu ya fadawa shugaba Muhammadu Buhari ya fito da kudi, ya daina matse aljihu yayin da miliyoyin matasa su ke cikin fatara a Najeriya.

Femi Gbajabiamila ya fada wa mai girma Muhammadu Buhari cewa ya dubi maganar da Tinubu ya yi, kuma ya yi amfani da shawarwarin da jagoran na APC ya bada.

Source: Legit.ng

Online view pixel