Rikicin PDP: Babu wanda ya isa ya kore ni daga PDP, inji wani babban jigon jam'iyyar

Rikicin PDP: Babu wanda ya isa ya kore ni daga PDP, inji wani babban jigon jam'iyyar

- Wani jigon jam'iyyar PDP a jihar Imo ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya koresa daga jam'iyyar.

- Ya ce ya bada tsawon rayuwarsa yana aiki a jam'iyyar, kuma yasan irin rawar da ya taka har jam'iyyar takai banten ta a zaɓen gwamnan jihar

- A cewarsa ba'a fahinci asalin zancen sa ba a kafafen sada zumunta, inda wasu suka fara kiran a kore shi daga jam'iyyar gaba ɗaya

Wani Dattijon babban jam'iyyar hamayya PDP, Chief Emmanuel Iwuanyanwu, yace babu wanda ya isa ya kore shi daga jam'iyyar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Iwuanyanwu, ya bayyana cewa ya ɗauki tsawon rayuwarsa a matsayin ɗan kwamitin amintattu wato (BOT).

KARANTA ANAN: Hadimin Buhari ya fara fallasa masu daurewa Boko Haram da Miyagun ‘Yan bindiga gindi

Ya kuma ce ya bada dukkan lokacinsa wajen ganin jam'iyyar ta samu nasara.

Iwuanyanwu, ya ce aikin da ya yi ma jam'iyyar ne ya taimaka ta samu nasarar lashe zaɓen gwamna a jihar Imo a zaɓen 2019 ɗin da ya gabata.

Ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamitin riƙo na ƙungiyar yan jaridu reshen jihar Imo a ofishinsa dake Owerri.

Jigon PDP ɗin ya ƙara da cewa ya ɗauki tsawon rayuwarsa a mamban BOT ne sabida babban burinsa ya kawo ma jam'iyyar cigaba.

Babu wanda ya isa ya kore ni daga Jam'iyyar PDP, inji wani babban jigon jam'iyyar
Babu wanda ya isa ya kore ni daga Jam'iyyar PDP, inji wani babban jigon jam'iyyar Hoto: @PDPImoHeartland
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Barayi Sun Yi Wa Beyonce Satar Kayayyakin Da Kuɗinsu Ya Kai Dala Miliyan Ɗaya

A jawabin da yayi, Iwuanyanwu, ya ce:

"Ni bance na yi nadamar zaɓen PDP lokacin zaɓen gwamnoni na 2019 ba, Kuma bance nayi nadamar zaɓen ɗan yankin Owerri ba. An fahimci zance na ba dai-dai ba a kafar sada zumunta, saboda haka naji wasu na kira da a kore ni daga jam'iyyar."

"Babu wanda ya isa ya kore ni daga PDP, ni mamban BOT ne kuma nasan irin aiki tuƙurun da nayi wajen ganin PDP ta yi nasara a zaɓen gwamnonin da ya gabata a jihar nan."

A nasa jawabin, shugaban kwamitin riƙo na NUJ, Precious Nwadike, ta ce ƙungiyar su na farin ciki da irin rawar da yake takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A wni labarin kuma Ameachi Ya Faɗa Abin Da Yasa Ya Tafi Nijar Ya Roƙa a Bari Nigeria Ta Gina Layin Dogo Zuwa Maraɗi Kyauta

Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri na Nigeria ya ce sai da ya tafi Nijar da kansa ya roke su su amince Nigeria ta gina layin dogo zuwa Maradi.

Ministan ya ce ya zama dole ya yi hakan ne domin yin layin dogon zai amfani Nigeria sosai wurin kasuwanci da inganta tattalin arziki.

Source: Legit.ng

Online view pixel