Hadimin Buhari ya fara fallasa masu daurewa Boko Haram da Miyagun ‘Yan bindiga gindi

Hadimin Buhari ya fara fallasa masu daurewa Boko Haram da Miyagun ‘Yan bindiga gindi

The Nation ta ce gwamnatin tarayya ta yi magana mai ban razanar wa game da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram da kuma masu garkuwa da mutane.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ta gano dangatakar da ke tsakanin ta’addanci Boko Haram da kuma ta’adin da ‘yan bindiga masu satar mutane su ke yi.

A cewar mai magana da bakin shugaban kasa, daga cikin masu taimaka wa wadannan miyagu akwai ‘yan canjin kudi da su ke da mutanensu a kasar ketare.

Mallam Garba Shehu yake cewa akwai hujjojin da ke nuna ana aiko wa shugabannin kungiyar Boko Haram kudi daga kasar tarayyar Larabawa watau UAE.

KU KARANTA: Ana samun zaman lafiya a Najeriya - Magashi

Garba Shehu ya gaskata maganar da shugaban kungiyar gwamnoni, Dr. Kayode Fayemi, ya yi game da wadanda su ke da hannu wajen garkuwa da mutane.

Shehu ya bayyana wannan ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani gidan talabijin a ranar Talata.

Hadimin shugaban kasar ya ce abin mamaki ne ga kowane ‘dan Najeriya ace a wuraren ibada ake rufa asirin wadanda su ka kashe ‘yan sanda da jami’an tsaro.

A cewar Garba Shehu, tuni jami’ai sun yi bincike, kuma za a fara yin ram da wasu daga cikin wadanda aka samu da hannu dumu-dumu a wannan danyen aiki.

Mai magana a madadin shugaban kasar ya ke cewa babu wanda za a rufa wa asiri idan gaskiya ta fito, ya ce ko da kuwa wadanda aka samu da laifin ‘yan siyasa ne.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace wani Fasto a Kaduna

Hadimin Buhari ya fara fallasa masu daurewa Boko Haram da Miyagun ‘Yan bindiga gindi
Hadimin Shugaban kasa, Garba Shehu
Asali: Facebook

“Akwai mutanen da yanzu haka aka kama su."

"Ana zarginsu da laifin taimaka wa ‘yan ta’adda da kudi.”

‘Yan canji su na aika wa ‘yan ta’adda kudi."

"Ana aiko kudi daga UAE. Ana kuma yin wannan danyen aiki a gida.”

“Ina fada maku idan mu ka kammala bincikenmu, mutanen Najeriya za su sha mamaki.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng