Bayan kwanaki 7 an sake samun gobara ta 2 da ta ci wata kasuwa a Jihar Katsina

Bayan kwanaki 7 an sake samun gobara ta 2 da ta ci wata kasuwa a Jihar Katsina

- Gobara ta yi barna a kasuwar Magamar Jibiya da ke jihar Katsina

- Wuta ta ci shagunan ‘yan kasuwa cikin dare a farkon makon nan

- Hakan na zuwa ne bayan an yi mummanar gobara a garin Katsina

An samu rahoton ncewa wata gobarar dare ta ci kasuwar Magamar Jibiya da ke garin Jibiya, jihar Katsina.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan gobara ta barke ne cikin tsakar dare, sannan ta dauki tsawon lokaci ta na ci, kafin a kashe ta.

Jaridar Katsina Post ta rahoto cewa wutan ta fara ci ne da karfe 4:00 na dare, ba a iya kashe ta ba sai bayan tsawon lokaci da safiya.

KU KARANTA: Gobara ta ci dukiyar mutane a kasuwar Katsina Central market

Kamar yadda rahoton ya bayyana, gobarar ta yi wannan barna ne a kasuwar ta Magamar Jibiya a ranar Litinin, 29 ga watan Maris, 2021.

Shaguna da kantunan Bayin Allah da yawa da su ka kone a sakamakon wannan hadari na wuta.

An yi asarar dukiyoyin da ba a kai ga kiyasace adadinsu ba. Amma jaridar ta ce an yi dace gobarar ba ta yi sanadiyyar mutuwar kowa ba.

Magamar Jibiya ta na daga Arewacin Katsina, ta yi bakin iyaka da garin Maradi a Jamhuriyyyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.

Bayan kwanaki 7 an sake samun gobara ta 2 da ta ci wata kasuwa a Jihar Katsina
Gobara a Jibiya Hoto: katsinapost.com.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Hadimin Gwamnan Katsina ya mutu bayan ya fadi a taron biki

Kawo yanzu ba mu samu labarin abin da ya haddasa wannan gobara ba. Jami’ai ba su kuma bayyana adadin shagunan da su ka kone ba.

Wannan ita ce babbar gobara ta uku da ta tashi a garin Katsina a cikin ‘yan kwanakin bayan nan.

Wuta ya barke a wani babban banki da ke garin Katsina, jihar Katsina. Haka zalika wuta ta ci babbar kasuwar ‘Central’ wanda ake ji da ita.

A makon jiya kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce za ta taimakawa ‘Yan kasuwar da gobara ta yi masu barna a jihar Katsina da kuma Zamfara.

Ministar bada tallafi ta umarci NEMA mai bada agajin gaggawa na kasa umarni ta taimaka wa wadanda gobarar ta jawo masu asarar dukiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel