Da duminsa: Shugaba Buhari ya shiga zama majalisar tsaron Najeriya
- Cikin shirye-shiryen tafiyar, Buhari ya ce zai gana da majalisar tsaro
- Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro ta fuskoki da dama
- Daga Boko Haram zuwa yan bindiga, da kuma masu barazanar ballewa daga kasar
Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar zaman tsaro a cikin fadar Aso Villa yanzu haka.
Ana zaman ne yayinda shugaban kasan ke shirin tafiya Landan, kasar Ingila domin duba lafiyarsa.
Daga cikin wadanda ke zaman akwai mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin jihar Boss Mustapha; Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi; shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno.
Hakazalika akwai shugaban hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor; shugaban Sojin kasa, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru; shugaban Sojin ruwa, Vice-Admiral Awwal Zubairu; da shugaban mayakan sama, Air-Marshal Ishiaka Oladayo Amao.
Sauran sune Sifeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu; Dirakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi; Dirakta hukumar Leken asiri, Ambasada Ahmed Rufao Abubakar.
DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta bada hutu ranar Juma'a da Litinin don murnar Easter
KU KARANTA: Ku mamaye bakin asibitin da Buhari zai kasance, Sowore ga 'yan Najeriyar Burtaniya:
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya fara zuwa duba lafiyarsa Landan tun kafin ya zama shugaban kasan Najeriya a 2015.
Shehu ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai lokacin da jirgin Buhari ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Asali: Legit.ng