Na kashe mahaifiyata saboda fasto ya ce mun mayya ce, ‘yar shekara 30
- Blessing Jimoh ta bayyana yadda ta kashe mahaifiyar da ta tsuguna ta haife ta
- Wacce ake zargin ta yi furucin ne yayin da ‘yan sanda suka gurfanar da ita a Ondo
- A cewarta, ta aikata hakan ne bisa umarnin da fasto dinta wanda ya ce mahaifiyarta mayya ce ya bayar
Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar ya nuna cewa jami’an ‘yan sandan reshen jihar Ondo sun kama wata mata mai shekaru 30, Blessing Jimoh bisa zargin ta da kashe mahaifiyar ta, Ijeoma Odo.
Legit.ng ta tattaro cewa Blessing ta ce ta kashe mahaifiyar ta ne da adda bayan wani fasto ya ce mayya ce.
KU KARANTA KUMA: APC ta yi ikirarin cewa ba ta taba sanin matakin da cin hanci da rashawa ya kai ba a Najeriya
Blessing, wacce aka gabatar tare da wasu masu laifi 11 a hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Akure, ta ce tana da’ ya’ya hudu kuma ta aikata laifin lokacin da suke aiki a gonar da ke yankin Ile-Iluji.
An tattaro cewa faston yana kan gudu.
Jaridar This Day ta kuma ruwaito cewa an gurfanar da wasu wadanda ake zargi da aikata laifuka wadanda suka hada da satar mutane, fashi da kuma lalata da mata.
Blessing ta ce: “Wani abu da ke damuna ne ya sa na kashe mahaifiyata. Ba na farin ciki da abin da na yi. Na yanka wuyanta da adda. Wani Fasto ne ya ce ita mayya ce kuma na je na roƙe ta. Mahaifiyata yar asalin jihar Enugu ce. Mun dade muna neman Fasto amma ba mu gan shi ba.”
Rahoton ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bolaji Salami, ya ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wacce ake zargin zuwa kotu.
KU KARANTA KUMA: NBS ta fitar da jerin basusukan da ake bin kowace jihar Najeriya yayin da ya kai N4.2tn
A gefe guda, wasu mahara dauke da bindiga sun kaddamar da wani hari a tsakar dare a garin Kojoli da ke karamar hukumar Jada a jihar Adamawa inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin biyu, jaridar Punch ta ruwaito.
Wani dan asalin garin, Dokta Umar Ardo, ya ce ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin karfe 1 na safiyar Lahadi kuma suka yi awon gaba da wasu fitattun mutane biyu bayan sun fatattaki 'yan banga da ke yankin.
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar ya ci tura, saboda layin wayarsa ba ya shiga.
Asali: Legit.ng