Ganduje ya karfafa yaki da rashawa a jihar Kano, Cewar Tinubu

Ganduje ya karfafa yaki da rashawa a jihar Kano, Cewar Tinubu

- Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano a kan yaki da rashawa

- Sanata Tinubu ya sanar da hakan a yayin kaddamar da gyararrun ofisoshin hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano

- Tinubu yace hakan zai matukar taimakawa wurin samar da Najeriyar maras rashawa da kuma mutunci a idon duniya

Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Gwamnan jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kan karfafa yaki da rashawa da yayi a jihar.

Tinubu ya sanar da hakan ne yayin kaddamar da gyararrun ofisoshin hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Idan za mu tuna, Tinubu ya isa jihar Kano ne wurin taron kwararru karo na 12, taron da ya shirya domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

KU KARANTA: Doka da tsoron Allah ne jagororinmu, sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa

Ganduje ya karfafa yaki da rashawa a jihar Kano, Cewar Tinubu
Ganduje ya karfafa yaki da rashawa a jihar Kano, Cewar Tinubu. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tinubu yayi bayanin yadda Najeriya za ta magance rashin tsaro da rashin aikin yi

"Ya ku 'yan Najeriya dake hange tare da fatan samun Najeriya da Afrika inda babu rashawa, yau na sadaukar muku da wannan," yace.

Tinubu yace tabbatar da irin wannan yanayin aikin zai taka rawar gani wurin tabbatar da cewa Najeriya ta zama kasa da sauran kasashen duniya ke mutuntawa "kasar da bata da nauyin rashawa."

A jawabinsa, Gwamna Ganduje ya jinjinawa shugaban hukumar, Barista Rimingado, tare da tabbatar da cewa zai tsaya tsayin daka wurin tabbatar da nasarar hukumar.

A wani labari na daban, shugaban ƙasar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya bayar da tabaccin cewa rundunar sojin haɗaka zasu iya kawo ƙarshen ta'addancin Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƙasar Chadin a ranar Asabar ya tabbatar da hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati a fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan ziyarar kwana daya da ya kawo.

Shugaban Chadin ya cigaba da bayyana yadda ta'addanci yake cigaba da ciwa kowa tuwo a ƙwarya musamman a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel a Afirika saboda MNJTF basu fara aiki a wuraren ba.

A cewarsa, ya tattauna da Shugaba Buhari akan MNJTF inda yace da zarar sojojin haɗin guiwar sun fara ayyukansu na tsawon shekara ɗaya zasu ci galaba akan ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel