Rundunar sojin hadin guiwa ta MNJTF za su iya kawo karshen Boko Haram, Idris Deby
- Shugaban kasar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya ce yana da yaƙinin rundunar sojojin haɗin guiwa zasu iya kawar da Boko Haram
- Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar ne yayin tattaunawa da manema labarai bayan ziyarar kwana ɗaya daya kawo wa Shugaba Buhari
- A cewar Itno, jami'an suna da dabaru da salo na musamman kuma sababbi da zasu yi amfani dasu wurin kawo ƙarshen ta'addanci
Shugaban ƙasar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya bayar da tabaccin cewa rundunar sojin haɗaka zasu iya kawo ƙarshen ta'addancin Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ƙasar Chadin a ranar Asabar ya tabbatar da hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati a fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan ziyarar kwana daya da ya kawo.
Shugaban Chadin ya cigaba da bayyana yadda ta'addanci yake cigaba da ciwa kowa tuwo a ƙwarya musamman a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel a Afirika saboda MNJTF basu fara aiki a wuraren ba.
KU KARANTA: Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki
KU KARANTA: Bidiyon Dangote kai tsaye tare da ma'aikatansa yana kara karfafa musu guiwa
A cewarsa, ya tattauna da Shugaba Buhari akan MNJTF inda yace da zarar sojojin haɗin guiwar sun fara ayyukansu na tsawon shekara ɗaya zasu ci galaba akan ta'addanci.
Itno ya bayar da yaƙininsa har yake ƙara bayyana cewa jam'an sun zo da sababbin dabaru na musamman ta yadda cikin sauƙi zasu cimma gaci tun daga yankuna zuwa iyakokin ƙasashe don kawo ƙarshen 'yan Boko haram da mayaƙan ISWAP har abada.
A cewarsa sun tattauna akan wasu matsalolin da suke addabar Najeriya da ƙasar Chadi a taron da sukayi.
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin fahimtar hoton da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gabatar masa a fadar shugaban kasan dake Abuja.
Tun a farkon makon nan, Buhari ya karba bakuncin Ganduje wanda ya nuna masa hoton gadar Muhammadu Buhari da za a yi a jihar Kano.
A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso yayi mamakin dalilin da zai sa a karba bashin N20 biliyan a kan aikin nan, wanda yace aikin gwamnatin tarayya ne.
Asali: Legit.ng