Doka da tsoron Allah ne jagororinmu, sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa

Doka da tsoron Allah ne jagororinmu, sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa

- Sabon shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa. yace tsoron Allah da bin dokoki ne za su yi masa jagora

- Matashin shugaban hukumar EFCC yace matukar wani yasa shi abinda bai dace ba, tabbas zai yi murabus

- Ya ce yaki da rashawa ba aikin EFCC bane kadai, dole yasa za su saka shugabannin addinai da na al'umma tare da wayar da kan jama'a

Zababben shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya jaddada mayar da hankalinsa wurin kakkabe dukkan rashawa a kasar nan inda yace doka da tsoron Allah ne jagororinsa.

Ya bayyana rashawa a matsayin mummunan lamarin dake hana cigaban kasar nan inda yace akwai bukatar a hada karfi da karfe wurin ganin bayanta a kasar nan.

Channels TV ta wallafa cewa, Bawa ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Maris 2021 a wata tattaunawa ta musamman da aka yi dashi a gidan talabijin na kasa na NTA.

KU KARANTA: Kyawawan hotunan bishiya mai shekaru 1400 dake fitar da ganye launin zinari

Ba zamu huta ba sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa
Ba zamu huta ba sai mun ga bayan rashawa a Najeriya, Bawa. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki

"Akwai bukatar mu sauya halayenmu a Najeriya. Muna da dabi'ar bautawa masu kudi a kasar nan amma bamu taba tambayar ta ina suka samo kudin ba.

"A kokarin nasarar yaki da rashawa, dole ne mu saka dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin addinai, yankuna da sauransu.

"Za mu mayar da hankali wurin tsananta wayar da kan mutane a kan su yi watsi da dukkan wani nau'in rashawa," ya jaddada.

Shugaban EFCC ya sha alwashin yaki da rashawa da dukkan karfinsa kamar yadda shari'a ta bashi, yace: "Zan cigaba da yin abinda ya dace. Hukumar dake karkashina za ta cigaba da kiyaye dokoki. Idan wani ya umarce ni in yi abinda bai dace ba, zan yi murabus."

Ya ce yaki da rashawa ba aikin mutum daya bane kuma bai dace a bar shi a hannun EFCC kadai ba. Yayi kira ga 'yan Najeriya da su daina bautawa rashawa da masu cin ta a kasar nan.

A wani labari na daban, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa, makiyaya da 'yan Boko Haram sun kulla wata yarjejeniya mai tsari a wasu yankuna na jihar Yobe inda 'yan Boko Haram ke horar da makiyayan dabarun yaki.

SaharaReporters ta tabbatar da cewa wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace 'yan ta'addan na karbar sa daya a kowanne shanu 40 da sauran kayan abinci daga makiyayan a matsayin haraji.

An gano cewa, wasu daga cikin makiyayan da suka hada da kananan yara, ana basu makamai tare da horar dasu ta yadda za su gudanar da hari na gaba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel