Gwamnatin Bayelsa ta ba Fulani Makiyaya wa'adin makwanni biyu su tattara komatsansu su bar jihar

Gwamnatin Bayelsa ta ba Fulani Makiyaya wa'adin makwanni biyu su tattara komatsansu su bar jihar

- Gwamnatin Bayelsa ta baiwa fulani makiyaya wa'adin kwanaki 14 su tattara shanun su su bar jihar

- Shugaban kwamitin kula da kiwon dabbobi na jihar ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron su da ƙungiyar Miyetti Allah

- Ya kuma yi gargadi cewa duk wanda aka kama bayan cikar wannan wa'adin to ya kuka da kansa.

Kwamitin kula da hada-hadar dabbobi na jihar Bayelsa ya baiwa makiyaya wa'adin makwanni biyu su tatttara kayansu su bar jihar.

Kwamitin ya bada umarnin ne ga ƙungiyar Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN) da sauran makiyaya dake jihar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wasu 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Fasinjoji a Osun, Sun nemi a biya 50 Miliyan

Shugaban kwamitin kuma kwamishinan aikin gona da ma'adanan ƙasa, Mr David Alagoa, ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan taron da kwamitin ya yi da ƙungiyar miyetti Allah ta yankin kudu maso kudancin Najeriya.

Ya kuma gargaɗi waɗanda abin ya shafa cewa, da zaran wa'adin ya cika, kwamitin bazai lamurci ganin shanu na tafiya a kafar su ba a faɗin jihar.

Alagoa, ya roƙi mazauna jihar da su yi hakuri, suna kan tattaunawa da ƙungiyar MACBAN, ya kuma ƙara da cewa ɗaya daga ciki abun da suka fara shine fitar da shanu daga jihar.

Gwamnatin Bayelsa ta ba Fulani Makiyaya wa'adin makwanni Biyu su tattara komatsansu su bar jihar
Gwamnatin Bayelsa ta ba Fulani Makiyaya wa'adin makwanni Biyu su tattara komatsansu su bar jihar Hoto: @Bayelsastategov
Asali: Twitter

A cewar sa wannan wata dama ce da gwamnati ta ba mutane don su yi amfani da ita wajen kasuwanci kamar buɗe wurin yin kiwon dabbobi ko su noma ciyawa su siyarwa masu kiyon shanu.

KARANTA ANAN: Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Lakaɗawa Duka Har Suka Zubarwa Wani Haƙoransa

A jawabin kwamishinan yace:

"Mun amince cewa mun basu wa'adin kwana goma su bar jihar, bayan kwanaki 14, wanda zai kama 10 ga watan Afrilu za mu fara cafke shanun su."

"Idan har kana da sha'awar kasuwancin shanu, gwamnan mu ya samar da kyakkyawar dama ta babban kasuwanci gareka. Idan kana da wuri kuma kana son kiyo to ka yi, idan kuma noman ciyawa zakayi ka siyarwa masu shanu, to kayi, wannan shine lokacin da ya kamata."

Shugaban MACBAN reshen jihar Bayelsa, Alhaji Mohammed Tukur, wanda ya yi jawabi a madadin yan uwansa ya bayyana godiyarsa da har gwamnatin Bayelsa ta bar makiyaya sukai kiwon a baya.

A wani labarin kuma Shehu Sani ya ba Jigon APC, Tinubu muhimmiyar shawara bayan ya kai shekaru 69

A makon nan ne ake bikin taya fitaccen ‘dan siyasar kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa.

Sanata Sani ya ba Tinubu shawarar ya dauko mai fassara masa Hausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262