Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu

Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu

- Gwamnan jihar Ondo ya caccaki masu rajin kafa haramtacciyar kasar Yarbawa ta Oduduwa

- Gwamnan ya bayyana cewa, ba wanda ya isa ya yi magana a madadinsu su mutanen kudu

- Ya kuma bayyana hanyar da ya kamata a bi idan ma raba kasar ake so a yi, dole ne a yi yarjejeniya

Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya ce wasu mutane kalilan ba su isa su iya shelar kafa "kasar Yarbawa" ba, ba tare da yin la’akari da babban muradin yankin kudu maso yamma ba, The Cable ta rahoto.

Sunday Adeyemo, wani shugaban matasa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ayyana Yarbawa a matsayin wata kasa ta daban kuma ya bukaci ballewar jihohin kudu maso yamma daga Najeriya.

Da yake tsokaci kan sanarwar a ranar Litinin, Akeredolu ya ce mutanen Ondo sun zabi ci gaba da zama a Najeriya, ya kara da cewa masu yada kafuwar Jamhuriyyar Oduduwa 'yan siyasa ne wadanda suka rasa madafun iko.

KU KARANTA: 'Yan bangan Amotekun sun sake kame wasu shanu sama da 300

Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu
Wasu tsiraru ba su isa su ayyana raba mu da Najeriya ba, in Akeredolu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da yake magana a ranar Talata lokacin da yake gabatarwa a wani shiri a gidan Talabijin na Channels, Akeredolu ya ce batun ballewar dole ne ya kasance yarjejeniya ba ra'ayin wasu gungun mutane ba.

Gwamnan na Ondo ya ci gaba da cewa wadanda ke neman ballewar ba za su ari bakin mutanen jiharsa ba.

“Wasu gungun mutane ne ke tayar da wannan batun; sun cancanci hakan. Kowa na da 'yancin nasa matsayin, amma idan ka zo kan batun kasa ko kuma son barin wani tsari, dole ne a samu yarjejeniya,” inji shi.

“Ba wanda zai iya tashi da kansa ya ce yana magana ne a madadin wasu.

"Waye ya basu wannan ikon? Ba mu taba ba da iko ga mutane su yi magana a madadinmu a kan wannan abu mai mahimmanci ba. Wannan shi ne abin da muke cewa.

“Wasu mutane ba za su tsaya wata rana kawai su ce mana, 'eh, muna son kafa kasar Yarbawa ba.’ Ta yaya? A ina muka zauna muka tattauna wannan? Tare da wa da wa? A daidai wane lokaci? Don haka, idan ba ku dama da kowa ba, ba za ku iya wakiltar mu ba.”

KU KARANTA: Oyedepo ga Musulman Kwara: Ku bar mana makarantunmu na mishan, ba a dole

A wani labarin daban, Kungiyar zamantakewar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hure, ta ce makiyaya ba za su kasance cikin wahala ba idan aka raba Najeriya.

Mai magana da yawun kungiyar, Saleh Alhassan, ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake gabatarwa a wani shirin jaridar Punch wato The Roundtable.

A cewarsa, gwamnonin arewa za su bunkasa harkar kiwon dabbobi idan suka daina samun "kudin mai" daga Gwamnatin Tarayya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel