Likitoci zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba

Likitoci zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba

- Ƙungigar Likitocin ƙasar nan NARD ta bayyana cewa zata tsunduma cikin yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya su haƙƙokin su ba

- Ƙungiyar ta baiwa gwamnati wa'adi zuwa ƙarshen watan Maris ta yi abinda ya kamata ko su shiga yajin aiki

- Kuma sun buƙaci abiya su ragowar albashin su da aka riƙe musu da kuma kuɗaɗen inshora ga likitocin da suka rasa rayuwarsu a bakin aiki.

Ƙungiyar likitoci mazauna ƙasar nan sun yi barazanar zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnatin ƙasar nan bata biya musu buƙatunsu ba.

Ƙungiyar tace zata saurari gwamnati daga nan zuwa ɗaya ga watan Afrilu idan ba'a biya musu buƙatun su ba zasu shiga yajin aiki, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan musayar wuta, 'yan sanda sun ceci mutum 5 da aka yi yunkurin garkuwa dasu a Kaduna

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar bayan babban taron ta na ƙasa, ƙungiyar ta bayyana cewa buƙatun nata sun haɗa da biyan likitoci albashin su da aka riƙe.

Da kuma biyan albashin watan Maris da muke ciki kafin 31 ga watan Maris ɗin.

Sauran buƙatun sun haɗa da: biyan mambobin ƙungiyar hakkoƙin su da suke bin bashi harda na watan Maris musamman na jihohi da kuma ma'aikatan lafiya na makarantun gaba da sakandire.

Da kuma biyansu kuɗaɗen su na aikin haɗari da suke yi, 50% na asalin albashin ma'aikatan lafiya da kuma kuɗaɗen su na COVID19 musamman a jihohin ƙasar nan.

Kungiyar Likitocin ƙasar nan zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba
Kungiyar Likitocin ƙasar nan zasu tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati bata biya musu buƙatunsu ba Hoto: @FlyingDoctoreNg
Asali: Twitter

Ƙungiyar likitocin na cikin gida NARD ta kuma yi kira da a canza shugaban likitoci na (MDCN) saboda gazawar sa wajen gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Hakan zai bada cikakkiyar damar aiwatar da gyaran tsarin likitocin cikin gida ba tare da wani tsaiko ba.

KARANTA ANAN: Tashin Hankali! Yan sanda Sun cafke Mambobin IPOB 16 da bindigu da Bama-Bamai

NARD ta kuma kara yin kira da biyan ragowar albashinsu na shekarun 2014, 2015 da kuma 2016 ga mambobinta dake makarantun gaba da sakandire, na jihohi, kamar yadda a kayi yarjejeniya da su a baya.

Hakanan kuma ƙungiyar ta yi kira da a biya kuɗaɗen inshora na ma'aikatan da suka rasa rayukansu a bakin aiki musamman waɗanda suka rasu saboda kamuwa da cutar korona.

Sannan kuma likitocin na buƙatar a gaggauta biyan kuɗaɗen bada horo na shekarar 2020 da 2021 ga mambobinta harda waɗanda ke aiki ƙarƙashin gwamnatocin jihohi.

A wani labarin kuma ‘Yan Majalisa sun amince a gina wata Jami’ar Tarayya a Garin Shugaban kasa

Majalisar wakilan tarayya ta amince da kudirin kafa jamMi’ar koyar da aikin gona a garin Funtua, jihar Katsina.

A makon da ya gabata ne majalisar wakilai ta bi sahun takwararta watau majalisar dattawa game da kafa jami’ar tarayyar a Funtua.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262