Madalla! Sarkin da Ka sace a Jihar Rivers ya samu Kuɓuta Bayan wata ɗaya

Madalla! Sarkin da Ka sace a Jihar Rivers ya samu Kuɓuta Bayan wata ɗaya

- Sarkin garin Ikuru dake karamar hukumar Andoni, jihar Rivers, wanda aka sace sama da wata ɗaya da ya gabata ya samu kuɓuta

- Sarkin Ikuru, Aaron Ikuru ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane ba tare da an biya kuɗin fansa ba kamar yadda mai magana da yawun sa ya faɗa

- Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da kuɓutar sarkin kuma ba tare da an biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa.

Aaron Ikuru, Sarkin garin Ikuru, ƙaramar hukumar Andoni, jihar Rivers, wanda aka sace kwanakin baya ya samu kuɓuta, kamar yadda PM News ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

Mai magana da yawun sarkin, Maurice Ikuru, ya tabbatar da dawowar sarkin a ranar Lahadin nan.

An dai yi awon gaba da Ikuru ne tun ranar 21 ga watan Fabrairu sa'ilin da ya halarci wani taro da yan uwansa.

Kuma a ranar da aka ɗauke shi, Wani babban malamin jami'a, Dr. Jones Ayuwo, wanda yana daga cikin 'yan uwan sarkin Ikuru ɗin shima aka sace shi.

An sace malamin jami'ar ne a ya yin da yake dawo wa daga wani taro da ya halarta a Andoni.

Sai dai mai magana da yawun sarkin na Ikuru, Maurice Ikuru, bai bada cikakken bayani kan yadɗa aka sako sarkin nasu daga hannun masu garkuwan ba.

Yadai tabbatar da cewa sarkin ya kuɓuta daga hannun waɗan da suka sace shi ranar Asabar da dare.

Madalla! Sarkin da Ka sace a Jihar Rivers ya samu Kuɓuta
Madalla! Sarkin da Ka sace a Jihar Rivers ya samu Kuɓuta Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

KARANTA ANAN: ‘Yan Najeriya na kashe sama da N1trn don kare kansu a duk shekara, in ji Kenny Martins

Maurice ya bayyana cewa an saki sarkin ne ba tare da wani sharaɗi ba kuma ba a biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa.

Shima mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta Rivers, Nnamdi Omoni, ya bayyana cewa "Sai dai mugode ma Allah a kan komai."

Hukumar su ta 'yan sanda na cikin matuƙar farin cikin fitowar sarkin.

A wani labarin kuma Ganduje Ya Gwangwaje Gwarazan Gasar Karatun Al-Kur'ani Na 2021 Da Naira Miliyan 5

Hassan Fage, Kakakin mataimakin gwamnan Kano ne ya bada sanarwar kyautar gwamnan ga gwarajan a ranar Asabar

Gwamnatin Kanon ta ce ta bada wannan ne a matsayin gudunmawarta wurin habbaka ilimin addinin musulunci a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262