Ganduje Ya Gwangwaje Gwarazan Gasar Karatun Al-Kur'ani Na 2021 Da Naira Miliyan 5

Ganduje Ya Gwangwaje Gwarazan Gasar Karatun Al-Kur'ani Na 2021 Da Naira Miliyan 5

- Gwamnatin Jihar Kano ta bawa gwarazan gasar karatun Al-Kur'ani na 2021 Naira miliyan 5

- Hassan Fage, Kakakin mataimakin gwamnan Kano ne ya bada sanarwar a ranar Asabar

- Gwamnatin Kanon ta ce ta bada wannan ne a matsayin gudunmawarta wurin habbaka ilimin addinin musulunci a kasar

Gwamnatin Jihar Kano, a ranar Asabar ta bawa waɗanda suka lashe gasar karatun Alkur'ani mai Tsarki na ƙasa da aka gama a Kano Naira miliyan biyu da rabi kowannensu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanarwar da kakakin mataimakin gwamnan jihar Kano, Hassan Fage a Kano ya ce Muhammad Gusau daga jihar Zamfara da Nusaiba Ahmed daga jihar Kano ne suka lashe gasar a bangaren maza da na mata.

Ganduje Ya Gwangwaje Gwarazan Gasar Karatun Al-Kur'ani Na 2021 Da Naira Miliyan 5
Ganduje Ya Gwangwaje Gwarazan Gasar Karatun Al-Kur'ani Na 2021 Da Naira Miliyan 5. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

A jawabin da ya yi wurin rufe taron da aka yi Jami'ar Bayero da ke Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce maza 180 da mata 190 daga johohin Nigeria 36 da Abuja ne suka fafata a gasar na kwanaki 9.

Gwamnan ya da samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna ya ce wadanda suka wakilci jihohin su a gasar sun fafata a ɓangarori da dama daga izu biyu har zuwa 60 tare da suka hada Tajwidi da Tafsiri.

"Mun bada Naira miliyan 2.5 ga wadanda suka lashe gasar a bangaren maza da mata. Inganta ilimin addinin musulunci na cikin abubuwan da gwamnatin mu ke bawa muhimmanci musamman abinda ya shafi karatu da hadar Al-Kurani a dukkan matakai.

KU KARANTA: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno

"Wannan shine dalilin da yasa muka kafa Hukuma ta farko a jihar Kano mai kula da Makarantun Koyar da Karatun Kur'ani da Islamiyoyi, wacce ta samu nasarori sosai a bangaren haɓaka ilimin musulunci," in ji shi.

Ya kuma bada tabbacin cewa jihar Kano za ta cigaba da goyon bayan Gasar Karatun Kur'anin na ƙasa tare da mika godiya ga Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto saboda shiryawa da kula da gasar karatun Alkur'anin a Nigeria.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel