Sabon shugaban hukumar EFCC, Bawa ya fadi abu 1 da zai iya sa ya ajiye aiki

Sabon shugaban hukumar EFCC, Bawa ya fadi abu 1 da zai iya sa ya ajiye aiki

- Abdulrasheed Bawa ya ce EFCC za ta bi doka muddin yana shugaban hukumar

- Bawa ya ce zai ajiye mukaminsa da zarar an bukaci ya yi abin da ya saba doka

- A shekarar nan ne aka nada Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC

Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ya yi magana game da abin da zai sa shi ya bar kujerar da yake.

Daily Trust ta rahoto cewa Mista Abdulrasheed Bawa ya sha alwashin yin murabus daga shugaban EFCC idan aka bukaci ya yi abin daa ya saba doka.

Da aka yi hira da Abdulrasheed Bawa a wani shiri a gidan talabijin na NTA na kasa, ya bayyana cewa zai bi doka wajen duk aikin da zai yi a kujerarsa ta EFCC.

KU KARANTA: Ba za mu yarda fetur ya tashi ba – NLC

Bawa ya ce yaki da rashin gaskiya nauyi ne da bai kamata a bar wa jami’an hukumar EFCC kadai ba.

Sabon shugaban na hukumar ya yi kira ga al’umma su daina ganin darajar bata-gari da mutane marasa gaskiya da su ka samu arziki ta hanyoyin da ba su dace ba.

“Mu na bukatar mu canza dabi’armu a Najeriya. Mun saba da bauta wa wadanda mutanen da su ke da dukiya a al’umma, amma ba mu tambayar silar arzikinsu.”

Mista Bawa yake cewa: “Wajen cin nasara a yaki da rashin gaskiya, mu na hada-kai da duk masu ruwa da tsaki, kamar jagororin addinai, shugabanni da dai sauransu.”

Sabon shugaban hukumar EFCC, Bawa ya fadi abu 1 da zai iya sa ya ajiye aiki
Abdulrasheed Bawa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Mahaukaciyar ambaliya ta na nan tafe a 2021 - NIHSA

“Za mu shiga wayar da kai domin a jawo hankalin mutane su kaurace wa duk wata hanyar rashin gaskiya.”

“Zan cigaba da yin abin da ya ke daidai. A karkashina, hukumar EFCC za ta cigaba da yin biyayya ga dokar kasa. Duk wanda ya tambaye ni in yi abin da nake jin ba daidai ba, ko ya saba wa doka, zan yi murabus, in ajiye aiki na.”

Kun samu rahoto cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya kafa hukumar EFCC a shekarar 2003 domin yaki da rashin gaskiya da masu damfarar jama'a.

Daga lokacin da aka kafa hukumar, Nuhu Ribadu, Farida Waziri, Ibrahim Lamorde, Ibrahim Magu, da Mohammed Abba duk sun rike ta kafin zuwan Abdulrasheed Bawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng