Da Ɗuminsa: Rundunar Soji Ta Fitar Da Sunayen Mutum 300 Waɗanda Suka Yi Nasara Da Ranar Tantancewa

Da Ɗuminsa: Rundunar Soji Ta Fitar Da Sunayen Mutum 300 Waɗanda Suka Yi Nasara Da Ranar Tantancewa

Rundunar sojojin Nigeria ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasarar samun shiga shirin bada horaswa na aikin soja na gajeren zango wato short service kwas na 47/2021 a shafinta na Twitter.

An umurci wadanda aka fitar da sunayensu su tafi tsohuwar ginin makarantar Bada Horon Dakarun Sojoji, NDA, da ke Kaduna a ranar Talata 6 ga watan Afrilun 2021.

Rundunar Soji ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara tare da ranar tantancewa
Rundunar Soji ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara tare da ranar tantancewa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar Manjo GAT Ochigbano, sakataren soji, wadanda suka gaza hallatar wurin bada horon har zuwa karfe 7 na yammacin ranar Laraba 7 ga watan Afrilun 2021, za su rasa gurabensu kuma za a maye gurbinsu da wadanda ke jadawalin 'yan ko-ta-kwana.

DUBA WANNAN: Zulum Ya Ce Ya Kamata Mulkin Nigeria Ya Koma Kudu a 2023

An umurci wadanda suka yi nasarar su zo da wadannan abubuwan:

  1. Takardun karatunsu na ainihi da takardar neman aiki na SSC 47 da suka fitar daga yanar gizo mai dauke da hoton fasfo dinsu
  2. Kwafi hudu na hotunansu sanya da 'suit' a tsaye ba tare da hula ba
  3. Fararen rigunana T shirt biyu (marasa zane) da gajerun wanduna launin shudi (guda biyu)
  4. Bakaken wanduna biyu
  5. Fararen takalmin canvas na motsa jiki (guda biyu) (Ba za a amince da takalman roba ba)
  6. Fararen zannuwan gado da gidajen fillo guda biyu
  7. Bargo guda daya (launin kore na sojoji ko grey)
  8. Cokali da kwanukan cin abinci
  9. Kayan saka wa na zaman gida ko suit (kala biyu)
  10. Jami'an soji da ke aiki su taho da wasikar samun izinin zuwa bada horon daga kwamandojin su.

KU KARANTA: A Karo na Biyu, Masu Garkuwa Sun Sace Jigon APC a Lokacin Da Ya Tafi Duba Gonarsa

DUBA CIKAKEN JERIN SUNAYEN A NAN

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Online view pixel